'Na Fi Iyayenku Kokari,' Trump Ya ba da Mamaki a Wajen Kamfen a Amurka
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta fi iyayen ma'aikatan masana'antar motocin kasar amfani ga rayuwarsu
- Trump ya danganta bunƙasar masana'antar motoci da harajin da ya kakaba kan motocin ƙasashen waje, yana mai sukar shugabannin ƙungiyar UAW
- Sai dai alkaluman gwamnati sun nuna cewa yawan ma'aikatan masana'antar motoci da na masana'antu ya ragu tun bayan da Trump ya hau mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Michigan, Amurka – Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi wa ma'aikatan masana'antar motoci a jihar Michigan abin alheri fiye da yadda iyayensu suka yi masu.
Trump ya yi wannan ikirari ne yayin da yake jawabi a cibiyar gwajin motocin kamfanin GM da ke Milford, a jihar Michigan, ƙasa da kwanaki 100 kafin wani zabe a kasar.

Source: Getty Images
CBS News ta wallafa a X cewa shugaban ya yi amfani da taron wajen kare manufofinsa kan masana'antar motoci tare da sukar shugabannin ƙungiyar ma'aikatan motoci ta UAW.
Trump ya soki shugaban UAW
Trump ya soki shugaban ƙungiyar UAW, Shawn Fain, saboda goyon bayan da ƙungiyar ta bai wa Joe Biden da Kamala Harris a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024.
Ya yi iƙirarin cewa da 'yan Democrat sun ci gaba da mulki, da masana'antar motoci ta Amurka ba za ta ci gaba da kasancewa yadda take ba.

Source: Getty Images
Trump ya kuma ce harajin da ya kakaba kan motocin ƙasashen waje ya taimaka wajen bunƙasa masana'antar motoci, yana mai cewa samar da manyan motoci da SUV na kamfanin GM ya ƙaru da kaso 20 cikin ɗari a shekarar 2026.
An nuna raguwar ma'aikata
Sai dai rahotanni daga Hukumar Kididdiga ta Ma'aikata ta Amurka sun nuna cewa yawan ma'aikatan masana'antar motoci da kayan haɗa motoci ya ragu da kusan kaso 4 cikin 100 a faɗin ƙasar idan aka kwatanta da watan Disamban 2024.
USA Today ta wallafa cewa a jihar Michigan, adadin ma'aikatan masana'antu ya ragu da kaso 2.5 cikin 100 a daidai wannan lokaci.
Trump ya kuma yi amfani da ziyararsa zuwa Michigan wajen nuna goyon baya ga ɗan takarar jam'iyyar Republican na kujerar majalisar dattawa, Mike Rogers, gabanin zaɓen da za a gudanar.
Ga bidiyon da Trump ya yi magana a kasa:
Maganar ƙarancin makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya musanta rahotannin da ke cewa ƙasar na fuskantar ƙarancin makamai da harsasai a yayin rikicin da ya shafi Iran.
Trump ya ce Amurka tana da makamai fiye da kowace ƙasa a duniya, yana mai mayar da martani kan rahoton da ya ce gwamnatin ta dakatar da wasu shirye-shiryen kai hare-hare saboda fargabar ƙarancin makaman kariya.
Rahotannin sun yi iƙirarin cewa jami'an tsaron Amurka sun nuna damuwa kan raguwar wasu muhimman makaman kariya, amma Trump ya nace cewa ƙasar na da isassun makamai fiye da buƙata.
Asali: Legit.ng

