Da Gaske Alkalin da Ya ba Tinubu Nasara a Kotu a Zaben 2023 Ya Makance?
- Wani shafin Facebook ya baza labarin da ke da'awar cewa alkalin da ya sanar da nasarar Tinubu a zaben 2023 ya makance bayan tiyata a London
- Bincike ya gano cewa hoton da aka sanya a cikin labarin na tsohon babban alkalin kasar Ghana ne, ba na wani alkali a tarayyar Najeriya ba
- bugu da kari, babu wani alkali mai suna 'Tsamma Abubakar' a cikin kwamitocin da suka yi shari'ar kara ta zaben shugaban kasa na 2023 a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An yada zarge-zargen da ya jawo hankalin mutane da yawa a ranar 3 ga watan Yuli, 2026, inda aka yi da'awar cewa alkalin da ya yanke hukuncin nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya makance.
Labarin ya nuna sunan alkalin a matsayin "Tsamma Abubakar," kuma ya yi iƙirarin cewa an yi masa tiyata ne a birnin London na England a lokacin da ya samu matsalar.

Source: Facebook
Binciken Dubawa ya nuna cewa a ranar 4 ga Yuli, 2026, labarin ya samu masu sharhi 4,000, wanda ke nuna yadda yake yaɗuwa a cikin sauri.
Hoton da aka yi amfani da shi
Masana sun fara binciken hoton da aka haɗa da da'awar ta hanyar da ake tantance hotuna a yanar gizo domin gano gaskiya.
Inda sakamakon ya nuna a fili cewa hoton ba na wani alkali na Najeriya ba ne, a'a, sifar tsohon babban alkalin Ghana, Gertrude Torkornoo ce aka yi amfani da ita wajen yaudarar masu karatu.
Bayan haka, an duba sunayen alkalai da suka yi aiki a shari'ar zaɓen shugaban ƙasa a kotun daukaka kara da kotun koli.
A kotun koli, alkalai bakwai da suka haɗa da Inyang Okoro, Adamu Jauro, Uwani Musa Abba Aji, Lawal Garba, I.N. Saulawa, Tijjani Abubakar, da Emmanuel Agim ne suka saurari karar.
A kotun daukaka kara kuma, kamar yadda Channels Television ta rahoto, alkalai sun haɗa da Haruna Tsammani, Justice Stephen Adah, Justice Misitura Bolaji-Yusuf, Justice Boloukuoromo Ugoh, da Justice Abba Mohammed.

Kara karanta wannan
Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027
Shafin Dirty Updates a Facebook na cikin shafukan sada zumunta da dama da suka wallafa labarin kafin tantance shi.

Source: Twitter
Babu wani alkali mai sunan
Daga cikin sunayen da aka jera, ba a samu "Tsamma Abubakar" a cikinsu ba, sai dai an kaddara cewa masu baza labarin sun ɓata sunan Haruna Simon Tsammani, wanda shi ne ya jagoranci kotun daukaka kara a 2023.
Bugu da ƙari, binciken ya kasa gano wani rahoto na gaskiya, sanarwa ta hukuma, ko bayanin da ya tabbatar cewa Tsammani ko wani daga cikin alkalai da suka yi shari'ar ya rasa ganinsa bayan tiyata a London.
Saboda haka, aka yanke hukunci da cewa da'awar makancewar alkalin da ya sanar da nasarar Tinubu a zaɓen 2023 ƙarya ce.
An zargi jami'an bola Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar CNPP ta zargi manyan jami'an gwamnatin Bola Tinubu da sakaci a harkokin gwamnati.
Hakan na zuwa ne bayan bankado ma'aikatar bogi da ta shafe shekaru tana aiki a Najeriya ba tare da sanin shugaban kasa da hukumomi ba.
A kan haka, CNPP ta bukaci manyan jami'an gwamnatin Bola Tinubu da abin ya shafa su ajiye aiki cikin mutunci ko kuma a kore su.
Asali: Legit.ng
