Peter Obi Ya Burma Matsala da Aka Bukaci Ya Biya N50bn

Peter Obi Ya Burma Matsala da Aka Bukaci Ya Biya N50bn

  • Mataimakin shugaban jam'iyyar LP na kasa, Abayomi Ararambi, ya zargi Peter Obi da bata masa suna bayan ya yi wasu kalamai a kansa
  • Abayomi Ararambi ya aika da wasikar gargadi kafin shigar da kara ga dan takarar shugaban kasar na NDC a zaben 2027
  • A cikin wasikar an zayyano jerin bukatun da ake nema daga wajen Peter Obi ciki har da kudade masu kauri da suka kai N50bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban jam'iyyar LP na kasa (shiyyar Kudu-maso-Yamma), Abayomi Arabambi, ya aike da wasikar gargadi kafin shigar da kara zuwa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi.

Ararambi ya bukaci Obi ya janye maganarsa a fili, ya ba shi hakuri, sannan ya biya shi Naira biliyan 50 a matsayin diyyar zargin kalaman batanci da ya yi masa a yayin wata hira.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Za a kai karar Peter Obi gaban kotu
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wannan bukata tana kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 3 ga watan Yuli, 2026, wadda kamfanin lauyoyi na Neplus Ultra Attorneys ya fitar.

Meyasa za a kai karar Peter Obi?

A cewar wasikar, matakin shari'ar ya samo asali ne daga kalaman da ake zargin Obi ya yi a lokacin wata hira, inda aka ce ya bayyana cewa Arabambi "ba shi da adireshi.", Arise News ta kawo labarin.

Tawagar lauyoyin Arabambi sun kafa hujjar cewa kalaman na shaci-fadi ne, na keta da kuma batanci, suna masu cewa kalaman sun nuna wanda suke karewa a matsayin mutumin da ba a san ko shi wanene ba, wanda ba shi da halacci sahihanci, ko mutunci a idon al'umma.

Lauyoyin sun jaddada cewa daga baya aka yada wannan hira a gidajen talabijin da kuma kafofin sada zumunta na zamani da dama, ciki har da Facebook, X, Instagram, TikTok, da WhatsApp, wanda hakan ya sa aka rika yi wa wanda suke karewa ba'a da dariya a idon duniya.

Kara karanta wannan

Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya

An bukaci Obi ya yi taka tsan-tsan

Wasikar ta ce:

"Wanda muke karewa yana da sanannen adireshin zama da na kasuwanci, yana da alaka ta kwararriyar alaka ta siyasa a cikin Najeriya, kuma bai taba kasancewa mutumin da ba a san inda yake ko kuma ko shi wanene ba."

A cewar lauyoyin, Obi, a matsayinsa na fitaccen dan siyasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, ya kamata ya nuna taka-tsantsan kafin ya yi kalaman da za su iya bata sunan wani mutum.

Wadanne bukatu suka nema?

A matsayin wani bangare na bukatunsu, tawagar lauyoyin Arabambi sun bukaci Obi da ya fitar da "janyewa a bayyane, kuma marar sharadi" na zargin kalaman batancin a cikin kwanaki bakwai da samun wasikar.

Lauyoyin sun kuma bukaci "ban hakuri a fili" wanda za a nuna shi a gidajen talabijin na kasa kuma a wallafa shi a shafukan sada zumunta na Obi, tare da buga gurbin ban hakuri na cikakken shafi a jaridun Vanguard, The Punch, The Guardian, THISDAY, da The Nation.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Peter Obi ya samu takardar gargadi
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Bugu da kari, Arabambi yana neman a biya shi naira biliyan 50 a matsayin diyya kan abin da ya bayyana da kushe ga mutuncinsa, darajarsa, matsayinsa na siyasa, da kuma kimarsa a idon jama'a.

Bayan haka, wasikar ta bukaci rubutaccen alkawari daga Obi na cewa zai guji yin duk wani karin kalaman batanci ga Arabambi nan gaba.

Tanadin da Peter Obi ya yi wa 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana tanadinsa na gina Najeriya mai albarka da ci gaba.

Obi ya tuna cewa tun lokacin da ya fara neman shugabancin ƙasa ya yi alƙawarin ɗora Najeriya kan turbar haɗin kai da sauyi mai ɗorewa.

Peter Obi ya ce zai mayar da hankali kan rage cin zarafin iko a gwamnati, dakatar da tabarbarewar rayuwar al'umma, da kuma samar da zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba da wadata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng