Mai Gidan Layla Othman Ya Zabi Ya Aika Mata Sako Gaban Duniya Ana Tsakiyar Runtsi

Mai Gidan Layla Othman Ya Zabi Ya Aika Mata Sako Gaban Duniya Ana Tsakiyar Runtsi

  • Yusuf Adamu Gagdi ya tuna da amaryarsa a rana irin ta yau da take murnar zuwan ta duniya
  • ‘Dan majalisar ya shaidawa duniya irin kaunar da yake yi wa Layla Ali Othman da ya aura a bara
  • An haifi fitacciyar ‘yar kasuwar ne karshen Junairu a shekarun baya, yau take cika shekara 38

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Soyayyar Yusuf Adamu Gagdi da sahibarsa Layla Ali Othman ta sake fitowa yayin da ta cika shekara 38 a duniya.

Rt. Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya yi amfani da ranar zagayowar haihuwar Hajiya Layla Ali Othman, ya aika mata sako a fili.

Layla Ali Othman
Layla Ali Othman da mijinta Hoto: Yusuf Adamu Gagdi PhD., OON
Asali: Facebook

‘Dan majalisar wakilan tarayyan ya yabi matarsa a shafin Facebook, yana mai godewa Allah SWT da ya hada shi da ita.

Kara karanta wannan

Matashi da ya mallaki naira miliyan 30 ya samu karayar arziki, ya koma rokon N2k

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Yusuf Gagdi ya yabi Layla Ali Othman

A cewar ‘dan majalisar na Najeriya, irinsu Layla Ali Othman ba su da yawa, yake cewa ta zama sukarin zamansa a duniya.

Idan za a tuna a shekarar da ta wuce ne aka ji ‘dan siyasar ya auri wannan ‘yar kasuwa da ta shahara a dandalin zumunta.

Wannan rana ta zagayo daidai lokacin da ake zargin wasu na neman bata mata suna.

A gefe guda kuwa, Hajiya Layla Othman ta wallafa hotunanta tare da iyalinta, ta ki kula masu surutu a game da rayuwarta.

Daga cikin halin kwarai da Yusuf Gagdi ya ambata na Layla Othman shi ne yadda take taimakawa marasa karfi a rayuwa.

Layla Ali Othman @ 38: Sakon Yusuf Gagdi

"Babu yadda zan nuna maki darajarki a rayuwa ta fiye da in yi maki fatan duk wani aheri a rayuwa a ranar murnar cikar ki shekara 38 da haihuwa."

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

"Ya matata abin kauna, ki cigaba da kasancewa ke din da na sani kuma ki ka saci zuciyata, yayin da na ke cigaba da addu’ar soyayyar da ta hada mu ta cigaba da tsirowa a zuciyarmu.”
"Mijinki, Rt. Hon. Dr Yusuf Adamu Gagdi PhD., OON."

- Yusuf Adamu Gagdi

Auren gata a Kebbi

Ana da labari Gwamnatin jihar Kebbi ta zakulo zauarawa da sauran mata da aka yi wa auren gata karshen makon da ya gabata.

An yi hakan ne domin rage lalata a gari ta hanyar rage yawan zauarawan da ke yawo a gari, da saukakawa maza da ke nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel