Yusuf Gagdi: Dan Majalisa Ya Bayyana Hukuncin da Ya Dace da 'Yan Ta'adda
- Yusuf Gagdi wanda ke wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a Majalisar Wakilai, ya nuna adawa kan shirin gyara halin 'yan ta'adda
- Dan majalisar ya bayyana cewa bai kamata ana daukar kudin jama'a ana kashe su wajen gyara halin 'yan ta'adda ba
- Yusuf Gagdi ya nuna cewa duk wanda ya dauki makami ya kashe rai, bai kamata ya sake samun damar ci gaba da rayuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Dan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam a Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi, ya nuna adawarsa ga shirin gyara hali ga yan tawaye da sauran miyagun masu laifi.
Yusuf Gagdi ya jaddada cewa duk wanda ya kashe wani da gangan ya kamata ya fuskanci hukuncin kisa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya yi wadannan kalaman ne a ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026 yayin da yake magana a gidan rediyon Silverbird Rhythm 93.7 FM da ke Jos.
Me Yusuf Gagdi ya ce kan rashin tsaro?
Gagdi, wanda dan asalin jihar Plateau ne, ya bayyana cewa duk wanda aka kama da laifin kisan kai ya kamata ya fuskanci hukuncin kisa maimakon tura shi shirin gyara hali.
Ya jaddada cewa bai kamata a kashe kudaden al'umma wajen gyara halin mutanen da ake zargi da karkashe bayin Allah ba, yana mai cewa irin wannan manufa tana gurgunta adalci kuma tana kasa hana aikata laifuffuka.
"Duk wani mai laifi, kowane mutum da ya dauki ran wani, bai kamata ma a tura shi shirin gyara hali ba tun farko."
- Yusuf Gagdi
Jami'an tsaro na dar-dar da tubabbun 'yan ta'adda
Dan majalisar ya kuma bayyana cewa wasu jami'an tsaro suna da fargaba game da yin aiki tare da tsofaffin yan tawaye da aka yi wa gyaran hali, inda ya yi zargin cewa an samu lokutan da wasu daga cikin wadanda aka mayar cikin al'umma suka rika satar bayanan sirri na ayyukan tsaro suna bai wa kungiyoyin masu laifi.

Kara karanta wannan
Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya
"A wasu lokutan, hukumomin tsaro suna kin yin wasu ayyukan saboda ba su yarda da mambobin Boko Haram da aka yi wa gyaran hali da ke tare da su ba."
"Akwai lokutan da wadannan mutane da ake kira wai an yi musu gyaran hali su ne mutanen da suke bai wa masu laifi bayanai a kan yadda za su yi wa tawagar hukumomin tsaro kwanton bauna."
- Yusuf Gagdi

Source: Facebook
Wane hukunci ya dace da su?
Gagdi ya ce bai yi amanna cewa ya kamata miyagun masu laifi, musamman yan tawaye, su amfana da irin wadannan tsare-tsare ba.
"To me zai sa na yi amanna da gyaran hali? Duk wanda ya yi kisa, a kashe shi. Shi ke nan. Idan da muna yin hakan, da hakan ya rage matsalar.
- Yusuf Gagdi
Gagdi ya yi zargi kan 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Yusuf Gagdi ya yi zargi kan wasu bangarori na ‘yan adawa dangane da matsalar rashin tsaro.
Yusuf Gagdi ya zargi wasu 'yan adawa da amfani da kalubalen tsaron Najeriya domin cimma manufar siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Ya bayyana cewa ko da yake rashin tsaro babban abin damuwa ne ga kasa, wasu ‘yan siyasa sun fi nuna sha’awar yin amfani da shi domin bata sunan gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng
