'Dan Majalisar Tarayya Ya Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Shirin Sauya Fasalin Aikin NYSC

'Dan Majalisar Tarayya Ya Bukaci Tinubu Ya Dakatar da Shirin Sauya Fasalin Aikin NYSC

  • 'Dan Majalisar wakilai, Hon. Philip Agbese ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na sake fasalin hukumar NYSC
  • Agbese ya yi gargadin cewa wasu daga cikin sauye-sauyen na iya raunana ainihin manufar da aka kafa NYSC a kanta
  • Kalaman Agbese na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta sanar da wasu manyan sauye-sauye a shirin matasa masu yiwa kasa hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Philip Agbese, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da aiwatar da sauye-sauye a hukumar NYSC.

Idan baku manta ba dai gwamnatin tarayya ta shirya yi wa Hukumar Yi wa Kasa Hidima ta Matasa (NYSC) garambawul, wanda ya kunshi canza khaki, tsarin gudanarwa da sauransu.

Philip Agbese.
Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilan tarayya, Hon. Philip Agbese Hoto: Philip Agbese
Source: Twitter

An hango matsala a gyaran NYSC

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nuna damuwa kan gargadin da Majalisar ɗinkin duniya ta yi wa Arewacin Najeriya

Premium Times ta ruwaito Hon. Agbese ya yi gargadin cewa wasu daga cikin sauye-sauyen na iya raunana ainihin manufar da aka kafa NYSC a kanta tare da rage muhimmancinsa wajen tabbatar da tsaron kasa.

Agbese, wanda ke wakiltar mazabar Ado/Okpokwu/Ogbadibo ta jihar Benue, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce duk da cewa gyare-gyare suna da muhimmanci domin sabunta shirin da ya dace da zamani, bai kamata su sauya manufar NYSC ta hada kan 'yan Najeriya, gina tarbiyya da kuma bunkasa kishin kasa ba.

Dan Majalisa ya ba Tinubu shawara

Agbese ya bukaci Tinubu da ya kafa wani kwamitin da zai hada da 'yan majalisa, masana harkokin tsaro, tsofaffin shugabannin NYSC, kungiyoyin matasa da masu ruwa da tsaki domin su yi cikakken nazari kan sauye-sauyen kafin a fara aiwatar da su.

A matsayinsa na mamba a kwamitocin majalisar kan harkokin matasa da tsaro, Agbese ya bayyana NYSC a matsayin daya daga cikin hukumomin kasa mafi dadewa da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina hadin kan kasa.

Ya ce duk wani yunkurin sake fasalin shirin dole ne ya kare manufofin da aka kafa shi a kai, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rahoton IMF: Atiku ya aika tambaya ga Tinubu kan 'wanda ke sace 2%' na kuɗaɗen Najeriya

Agbese ya yi fatali da wasu sauye-sauye

Kalaman Agbese na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta sanar da wasu manyan sauye-sauye ga NYSC, wanda Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana a matsayin gyara mafi girma tun bayan kafa hukumar.

Ministan ya ce an tsara sauye-sauyen ne domin sabunta NYSC tare da daidaita ta da bukatun tattalin arziki da ci gaban kasa.

NYSC .
Matasa masu yiwa kasa hidima suna rantsuwar kama aiki a sansanin hukumar NYSC Hoto: @NYSC
Source: Getty Images

Sai dai Agbese ya ce bai kamata a mayar da NYSC wata cibiyar koyon sana'a kadai ba.

Ya ce:

"Mayar da NYSC cibiyar koyon sana'a kawai ba zai amfani rayuwar kasa ba."

A cewarsa, shirin NYSC ya dade yana taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasa a lokutan bukata, musamman a bangarorin ilimi, lafiya, gudanar da zabe da sauran ayyukan gwamnati.

Dalilin sauye-sauye a hukumar NYSC

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta amince da gyare-gyaren da aka yi wa tsarin yi wa kasa hidima na NYSC.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta shiga batun ma'aikatar bogi, ta aika sako ga gwamnatin Tinubu

Tinubu ya ce gyare-gyaren na da nufin wadatar da matasan Najeriya da fasahohin aikace-aikace da kuma shirya su domin ci gaban kasa.

Ya ce ko da yake NYSC ta yi aiki don tabbatar da hadin kan kasa na tsawon shekaru sama da 50, sauye sauyen da aka samu a halin yanzu a kasar suna bukataer sabuwar hanyar tafiyar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262