'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Tinubu Ya Shirya Amfani da Fasahohin Zamani a Najeriya
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ƙara kaimi wajen amfani da sababbin fasahohi wajen yaƙi da rashin tsaro
- Tinubu ya bayyana cewa ana zuba jari wajen sayen kayan aikin sojoji na zamani da horas da jami'ai domin murkushe duk wata barazana
- Gwamnan jihar Ribas karkashin jagorancin Gwamna Siminalayi Fubara da Hafsan Sojin Ƙasa sun yabawa jami'an soji kan ƙoƙarinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalar tsaro ta hanyar amfani da sababbin fasahohi na zamani.
Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da fasahohin zamani, ayyukan tattara bayanan sirri da kuma ci gaba da inganta rundunar sojojin Najeriya domin dawo da zaman lafiya.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya Litinin yayin rufe bikin ranar Sojojin Najeriya ta 2026 da kuma taron African Land Forces Forum (ALFF) da aka gudanar a Fatakwal, jihar Ribas.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya wakilci shugaban ƙasar a wajen taron.
Gwamnatin Tinubu na ƙarfafa rundunar soji
A cewarsa, gwamnatinsa na ci gaba da zuba jari wajen samar da kayan aikin soja na zamani da kuma horas da dakarun domin inganta shirye-shiryen yaƙi da ƙara ƙarfafa shirinsu na fuskantar barazanar tsaro.
Ya ce:
"Gwamnatina ta himmatu wajen yaƙar sababbin barazanar tsaro ta hanyar amfani da fasahohi na zamani da kuma ƙarfafa ƙwarewar jami'anmu a dukkan fannonin aiki."
Njeriya za ta ƙara ƙera kayan aikin soja
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin bincike, ƙirƙire-ƙirƙire da samar da kayan aikin sojoji a cikin gida, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.
Ya bayyana cewa farfaɗo da masana'antar kera makaman sojoj (DICON) na da nufin bai wa Najeriya damar ƙera kayan aikin tsaro da kanta tare da rage dogaro da ƙasashen waje.
Shugaban ya bayyana taron African Land Forces Forum a matsayin wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen Afirka, bunƙasa diflomasiyyar tsaro da kuma musayar ilimi da ƙwarewa.
Zaman lafiya ya dawo Ribas
Tun da farko, gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce karɓar baƙuncin taron ya nuna cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo jihar.
Gwamnan ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara kula da walwalar jami'an rundunar sojoji.

Source: Twitter
Shi ma Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sake tabbatar da aniyar rundunar sojojin Najeriya na kare yankunan ƙasar da rayuka da dukiyoyin al'umma duk da sauye-sauyen barazanar tsaro.
Tinubu na zuba ayyuka a Arewa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya na da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa.
Mai giram Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na kan gudanar da ayyukan tituna 61 a wannan yaki kuma ana sa ran za su inganta rayuwar al'umma.
A cewarsa, jihohin yankin ba su taba cin gajiyar irin wannan gagarumin shirin raya ababen more rayuwa daga gwamnatin tarayya kamar yadda ake yi yanzu ba.
Asali: Legit.ng

