Da Taimakin Gwamnatin Abba Kabir, An Yi Sulhunta Ƙungiyoyin 'Yan Daba a Jihar Kano
- Wata ƙungiya ta sasanta rikicin kungiyoyin ‘yan daba a jihar Kano domin rage tashe-tashen hankula
- Bayan sulhun da aka yi da tallafin gwamnatin Kano, an kuma fara rajistar matasan da ke cikin daba da shaye-shaye domin koyon sana’a
- Kungiyar ta bukaci masu hannu da shuni su taimaka wajen farfado da rayuwar matasan domin ceto su daga aikata mugayen laifuffuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ƙungiyar Arewa Youth Merger Group (YMG) ta sasanta rikicin ƙungiyoyin ‘yan daba masu gaba da juna a jihar Kano.
Hakan wani bangare ne na wani yunƙurin kawo ƙarshen tashin hankali, ƙwacen wayoyi, shaye-shaye da fashi da makami a sassan jihar Kano.

Source: Facebook
Leadership ta ce shirin sulhun ya samu goyon bayan hukumomin tsaro, ƙungiyoyin matasa, sarakunan gargajiya da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano za ta taimaki yan daba
Yayin taron sulhun, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Hon. Musa Mujahid Zaitawa, ya ƙaddamar da rabon fam ɗin rajista ga matasa marasa aikin yi da ke cikin harkar daba da shaye-shaye.
Ya bayyana cewa za a miƙa sunayen waɗanda suka yi rajista ga gwamnatin jihar Kano domin ba su horon sana’o’i tare da tallafin jari, domin su samu hanyar dogaro da kai ta halal.
A cewarsa, harkar daba na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a Kano, yana mai cewa bai wa matasa ilimi da sana’a zai taimaka sosai wajen rage aikata laifuffuka.
Ana so Dangote da attajirai su tallafa
Mujahid Zaitawa ya yi kira ga fitattun attajiran Arewa da suka haɗa da Aliko Dangote, Abdussamad Isyaku Rabiu, A.A. Rano, A.Y. Maikifi, Bashir Dankullu, Sabiu Bako, Bureza, Danlami Alasan, Hamisu Dankaka da Yahaya Lawan.
Haka kuma ya buƙaci kamfanoni irin su Mudassir and Brothers da Garba Karfe Investment da su haɗa hannu da ƙungiyar wajen tallafa wa shirin gyaran rayuwar matasan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun shiga uku, Tinubu ya shirya amfani da fasahohin zamani a Najeriya
Ya gargaɗi iyaye da ‘yan siyasa
Shugaban ƙungiyar ya buƙaci iyaye su ƙara sa ido kan ‘ya’yansu domin dakile matsalar shaye-shaye da aikata miyagun laifuffuka.
Ya kuma gargaɗi ‘yan siyasa da kada su riƙa amfani da matasa wajen tayar da rikici yayin yaƙin neman zaɓen shekarar 2027.
Har ila yau, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su hukunta duk wani matashi da aka sasanta amma ya koma aikata laifi.
Yan sandan sun kama motoci 81 a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Kano ta kama motoci 81 masu lambar rajista da aka rufe, aka lalata ko kuma marasa rajista saboda matsalolin tsaro.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata.
CP Bakori ya ce rundunar ta lura da karuwar motocin da ke amfani da lambobin rajista da aka rufe ko aka lalata domin ɓoye.asalinsu.
Asali: Legit.ng
