Tinubu Ya Gaji da Jira, Ya Tura Bukatar Kirkirar 'Yan Sandan Jihohi ga Majalisa

Tinubu Ya Gaji da Jira, Ya Tura Bukatar Kirkirar 'Yan Sandan Jihohi ga Majalisa

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Majalisar dattawa da ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin inganta tsarin tsaro a Najeriya
  • Tinubu ya ce kudirin zai sauya kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sanda karkashin tsarin doka na kasa
  • Majalisar Dattawa ta mika kudirin shugaban kasar ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki domin duba shi da daukar mataki na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa da ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a fadin Najeriya

Bukatar shugaban kasar na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da ranar 15 ga watan Yuni, 2026, wadda Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta a zauren majalisar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso da batun 'karfin iko' yayin da ake shirin kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dattawa kudurin kirkirar 'yan san jihohi.
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a zauren hadin gwiwa na majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Dalilin son kafa ‘yan sandan jihohi

A cikin wasikar, Tinubu ya bayyana cewa kudirin dokar gyaran kundin tsarin mulki kan kafa ‘yan sandan jihohi na shekarar 2026 na neman sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 domin samar da tsarin doka ga kafa rundunonin ‘yan sanda a jihohi, in ji rahoton The Nation.

Shugaban kasar ya ce kudirin na da nufin magance sauye-sauyen kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta ta hanyar samar da tsarin ‘yan sanda guda biyu, wato na tarayya da na jihohi.

A cewarsa, sabon kudurin zai bai wa rundunonin tsaro damar aiki cikin tsari da kundin tsarin mulki ya amince da shi domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Tinubu ya bayyana cewa kudirin ya ginu ne kan kokarin da majalisun tarayya suka fara a baya, tare da kara wasu matakai na kariya domin tabbatar da aiwatar da shi yadda ya kamata.

Ya ce:

“Wannan kudiri ya ginu ne kan gagarumin aikin da majalisar wakilai da majalisar dattawa suka riga suka yi a wannan bangare, tare da kara wasu matakan kariya domin kafa tsarin ‘yan sanda biyu da zai taimaka wajen magance kalubalen tsaron kasa.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta tanka da Peter Obi ya nemi Tinubu ya yi murabus

Shirin sauya tsarin tsaron Najeriya

Tinubu ya bayyana kudirin a matsayin wani muhimmin bangare na shirin gwamnatinsa na sake fasalin tsarin tsaron Najeriya domin inganta kariyar jama’a.

Ya ce tsarin zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya. Shugaban kasar ya bukaci sanatoci su yi gaggawar duba kudirin tare da daukar matakin da ya dace.

Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta gaggauta amincewa da kudurin kirkirar 'yan san jihohi.
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a zauren hadin gwiwa na majalisar tarayya a Abuja. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Matakin da Majalisar dattawa ta dauka

Bayan karanta wasikar shugaban kasa, Akpabio ya mika kudirin ga kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki domin ci gaba da aikin duba shi.

Shugaban majalisar dattawan ya umarci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa ranar Laraba domin daukar matakin gaggawa, in ji rahoton The Cable.

Ya kara da cewa da zarar an gabatar da rahoton, za a duba shi a zauren majalisar baki daya domin hanzarta kammala aikin kafin tafiya hutun majalisa.

Martanin gwamnoni kan 'yan sandan jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa gwamnoni sun fara neman a kara masu karfin iko a harkokin tsaro yayin da ake kokarin kafa rundunar yan sandan jihohi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun fadi wasu matakai da suka dauka da aka fara zaben gwamnan Ekiti

Hakan na kunshe a cikin rahoton bayan taro da Antoni Janar na jihohi suka gudanar a sakatariyar kungiyar gwamnoni da ke Abuja.

Rahoton ya nuna cewa mahalarta taron sun yi nazari kan wasu tanade-tanaden da ke gaban Majalisar Tarayya musamnan kan ikon gwamnoni.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com