Rahoton IMF: Atiku Ya Aika Tambaya ga Tinubu kan 'Wanda ke Sace 2%' na Kudaden Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar ya sake caccakar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ake kashe kudin jama'a
- Atiku ya bukaci Tinubu ya yi wa yan Najeriya karin haske kan rahoton IMF da ya nuna 2% na tattalin arzikin Najeriya na sulalewa
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce lamarin ya wuce kuskuren lissafi kawai, dole akwai wani boyayyen al'amari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi cikakken bayani kan abin da ya kira "batan kashi 2%' na Tattalin Arzikin Kasa (GDP).
Hakan na zuwa ne bayan Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa an kashe kudaden gwamnati da suka kai 2% ba tare da sanya su cikin kasafin kudin kasa ba.

Source: Facebook
Atiku ya nemi gwamnatin Tinubu ta fito ta yi bayani a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 4 ga watan Yulin 2026.
Atiku ya ce bayanin da IMF ya yi, tare da ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye hukumar PFIPC da ake zargin ta bogi ce, na nuna akwai tsarin cin hanci da rashawa da ya yi katutu a gwamnatin tarayya.
Atiku Abubakar ya bukaci karin haske
Atiku ya ce rashin sanya irin wannan babban kaso na kudaden gwamnati cikin kasafin kasa ya haifar da manyan tambayoyi na kundin tsarin mulki, doka da kuma gaskiya.
Ya ce:
"Kundin tsarin mulki ba littafin shawarwari ba ne. Sashe na 80 ya bayyana karara cewa ba za a cire kudi daga asusun tarayya ba sai yadda Majalisar Tarayya ta amince. Kasafin kudi shi ne tushen doka na duk wata mu'amala ta kashe kudi da gwamnati ke yi."
"Idan har kamar yadda IMF ya bayyana, an kashe kudaden da suka kai kashi 2% na GDP ba tare da sanya su cikin kasafi ba, to 'yan Najeriya na da hakkin tambayar abu guda daya: Wa ya sace wannan kaso 2% na GDP din Najeriya?"
Atiku ya kore batun kuskuren lissafi
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce lamarin ya wuce kuskuren lissafi kawai, dole akwai wani ɓoyayyen al'amari.
A cewarsa:
"Wannan ba kuskuren kididdiga ba ne. Babban abin kunya ne da ya shafi kundin tsarin mulki, doka da kuma gaskiya, kudi ba sa bacewa daga kasafin kasa haka kurum.
Ya danganta lamarin da PFIPC
Atiku ya ce bayanan IMF sun kara tabbatar da cewa batun PFIPC ba wani lamari ne daban ba, illa wani bangare na matsalar yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati.
Atiku ya ce babu wata hukuma da za ta samu amincewar gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da izini daga matakin koli ba.

Source: Facebook
Saboda haka ya bukaci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya fito ya bayyana yadda aka amince da hukumar PFIPC da ake ta cece kuce a kanta.
Atiku ya ce al'amarin ya wuce siyasa, yana mai kira ga Majalisar Tarayya da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su gudanar da bincike.
Atiku ya yi magana kan hukumar bogi
A baya, an ji cewa dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sanya a gudanar da bincike kan hukumar bogi da ake ta surutu a kanta.
Atiku ya yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai ƙara rura wutar zargin jama'a na cewa wasu manyan mutane masu iko a gwamnati sun ci gajiyar lamarin.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa bayanan da fadar shugaban kasa ta yi, ba su warware shakkun da ake da shi kan lamarin ba.
Asali: Legit.ng


