Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun 'Yan Fashi da Makami a Gombe

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun 'Yan Fashi da Makami a Gombe

  • Dubun wasu hatsabiban 'yan fashinda makami ta cika bayan sun fada komar 'yan sanda a jihar Gombe
  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Gombe sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan samun rahoto kan barnar da suka yi
  • 'Yan sanda sun titsiye daya daga cikinsu wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga cafke sauran mambobin kungiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Gombe - Rundunar 'yan sandan jihar Gombe ta kama mutane takwas da ake zargi da kasancewa mambobin wata kungiyar masu laifi.

Ana zargin ne mutanen ne da hannu a fashi da makami da kuma damfarar intanet a wasu garuruwa da dama a jihar Gombe.

'Yan sanda sun cafke miyagu a Gombe
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rahoton jaridar The Punch ya nuna cewa an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan bincike kan wani lamari na fashi da aka bayar da rahotonsa a ranar 7 ga Yuni, 2026, a Wuro Birji, a karamar hukumar Akko.

Kara karanta wannan

Mutanen da 'yan bindiga suka sace a wurin Ibada sun dawo gida, mutum 1 ya mutu a Ekiti

Yadda 'yan fashi suka shiga hannun 'yan sanda

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, 5 ga watan Yulin 2026.

Wadanda abin ya shafa Hassan Muhammad da Jibril Hassan, sun ba da rahoton cewa wasu mutane dauke da makamai da takubba sun shiga gidajensu kuma suka sace wayoyinsu na hannu.

Yan sandan sun ce daga baya wadanda ake zargin sun yi amfani da bayanan da suka samu daga na'urorin da aka sace domin samun damar shiga asusun banki na wadanda abin ya shafa ba tare da izini ba.

Sun dade suna tafka ta'asa

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun cire N296,790 ta hanyar zamba daga asusun GTBank na daya daga cikin wadanda abin ya shafa, sannan kuma sun karbi tare da cire wani bashi na N205,205, wanda ya sanya jimillar kudaden da aka sace ya haura N500,000.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Sakamakon aiki da sahihan bayanan sirri da kuma bin diddigin fasaha na gaskiya kan harkokin kudaden na zamba, jami'ai sun yi nasarar gano wata ma'amala zuwa asusun Moniepoint, wanda hakan ya kai ga kama wanda ake zargi na farko, Mustapha Kabiru, wanda aka fi sani da 'Musty Bobo,' dan shekara 19, dalibin ND II a fannin kimiyyar Kwamfuta na kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya, Kaltungo."

Yan sandan sun ce Kabiru ya amsa laifinsa yayin tambayoyi cewa ya yi amfani da bayanan da aka samu daga wayoyin hannu da aka sace domin shiga asusun banki na wadanda abin ya shafa da kuma yin harkokin kudi na zamba.

'Yan sanda sun kama 'yan fashi a Gombe
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Daga baya, amsa laifinsa ya kai ga kama wasu karin mutane bakwai da ake zargi," in ji sanarwar.

A cewar rundunar, bincike ya kara bayyana cewa kungiyar ita ce ke da alhakin faruwar abubuwa makamantan haka sama da 13 a garuruwan Wuro Birji, Riyal, Bomala da Jauro Jatau.

Kara karanta wannan

Sufeton ƴan sanda ya ja kunne kan zargin an boye masu laifi a gidan gwamnatin Osun

Yan sandan sun ce bincike yana nan daf da kammalawa, yayin da aka tsananta kokarin kamo sauran mambobin kungiyar da har yanzu suka tsere.

'Yan bindiga sun kori mutane a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun jawo mutanen aƙalla ƙauyuka 30 a jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu.

Mutanen sun gudu ne biyo bayan hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa akai-akai a kauyukansu inda suke yi masu barna.

Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Gidan Gadanga, Gidan Dan Bube, Dutsin Mai Gunya, Batsauje, Sire Modi, Gwantsi, Kore Maiganga, Bangi Rafi, Bangi Dutsin, Yabawa, Lageji, Bille, Gonin Gari, Wumumu da Chohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com