'Yan Bindiga Sun Kori Mutanen Kauyuka a Sokoto, Manya Sun Dauki Mataki
- 'Yan bindiga sun kwashe kwanaki biyu suna kai hare-hare a wasu kauyukam da ke karamar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto
- Hare-haren na 'yan bindiga sun jawo mutanen kauyuka da dama sun tsere daga matsugunansu domin tsira da rayukansu
- Wasu mutane sun rasa rayukansu yayin da 'yan bindigan suka kuma yi awon gaba da dabbobin kiwo sama da guda 1000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Sokoto - 'Yan bindiga sun jawo mutanen aƙalla ƙauyuka 30 a gundumar Danchadi da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu.
Mutanen sun gudu ne biyo bayan hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa akai-akai, kamar yadda wani rahoto da mahukuntan gundumar suka ƙaddamar ya bayyana.

Source: Original
Rahoton, wanda jaridar Daily Trust ta samu, ya samu sa hannun Hakimin Danchadi, Alhaji Lirwanu Mafaran Kuwarun Sarkin Musulmi, kuma an aike da shi zuwa ga shugaban karamar hukumar Bodinga.
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Sokoto
Hare-haren, waɗanda suka auku tsakanin Laraba, 1 ga watan Yuli da Alhamis, 2 ga watan Yuli sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, sun raba daruruwan mazauna muhallansu, sannan sun yi sanadin sace fiye da dabbobi 1,000.
Haka kuma, an tura kwafin rahoton zuwa ga DPO jami’in shiyya na hukumar NSCDC, da kuma DSS na yankin.
Rahoton, wanda ke ɗauke da kwanan wata 3 ga Yuli, 2026, ya bayyana cewa ’yan bindigan sun kashe mazauna yankin guda shida a al’ummomin Kyaluje da Dibarke, sannan suka sace dabbobi fiye da 1,000, da suka haɗa da shanu da rakuma, yayin hare-haren.
An mika rahoto ga hukumomi
Wani babban basaraken gargajiya a gundumar, wanda ya yi magana bisa sharadin sakaya sunansa, ya tabbatar da rahoton, inda ya bayyana cewa shi da kansa ya kai kwafin rahoton ga wasu hukumomin tsaro da ke aiki a yankin.
Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Gidan Gadanga, Gidan Dan Bube, Dutsin Mai Gunya, Batsauje, Sire Modi, Gwantsi, Kore Maiganga, Bangi Rafi, Bangi Dutsin, Yabawa, Lageji, Bille, Gonin Gari, Wumumu da Chohi.
Sauran sun hada da Saran Malan, Wure Yal’dde, Gidan Hodi, Dabugi, Rukusawa, Tunga, Lakes, Maikataru, Dutsin Toka, Karaje, Kwantsi Buga, Yan Gidaje, Runbuki, Kwantsi Tunga da kuma Lau Gari.

Source: Facebook
Hakimin ya yi kira da a gaggauta kawo dauki na gwamnati domin dawo da tsaro da kuma ba da damar mazauna da suka tsere su koma kauyukansu.
Daruruwan mazauna yankin sun tsere zuwa garuruwan Danchadi, Bodinga da Sifawa, inda da yawa daga cikinsu ke fakewa a makarantu da gidajen dangi.
'Yan bindiga sun kashe tsohon soja
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kashe wani tsohon jami'in rundunar sojin Najeriya tare da sace wata mata.
Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon sojan ya rasa ransa bayan wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wata unguwa da ke iyakar Abuja da Nasarawa.
Maharan dai sun harbe Reuben Yelwa har ya mutu a wurin yayin da yake ƙoƙarin taimaka wa mazauna yankin da harin ya rutsa da su.
Asali: Legit.ng
