Adeyemi: Wanda Ake Zargi sa Kafa Ma'aikatar Bogi Ya Yi Zarge Zarge kan Gwamnatin Tarayya
- Shugaban hukumar PFIPC da gwamnati ta ce ta bogi ce, Adeniyi Adeyemi, ya shiga buya bayan abubuwan da suka faru
- Adeniyi Adeyemi ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin hatsari domin gwamnati na kokarin rufe masa baki
- Kalamansa dai na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zai fuskanci tuhume-tuhume guda takwas a gaban kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Adeniyi Adeyemi, mutumin da ake zargi da ƙirƙirar takardun naɗin bogi na gwamnati kuma yake nuna kansa a matsayin shugaban hukumar PFIPC, ya yi zargi kan gwamnatin tarayya.
Adeniyi Adeyemi wanda ya yi magana daga ɓoye, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa tana ƙoƙarin rufe masa baki ne kawai.

Source: Facebook
Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Premium Times a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026.
Me Adeyemi ya ce kan gwamnati?
Ya musanta aikata wani laifi kuma ya ce matakan da gwamnati ke ɗauka sun zama kawai kokarin kare kanta take yi.
"Kuna da masaniyar irin gwamnatin da muke da ita. Suna amfani da hanyar kariya ne kawai don su rufe mini baki. An kafa ƙungiyata ne a shekarar 2024."
- Adeniyi Adeyemi
Lokacin da aka buƙaci a haɗu da shi ido-da-ido don ya bayyana nasa labarin, Adeyemi ya ce ba ya cikin Abuja.
Adeyemi ya ki kawo hujja
Haka kuma ya ƙi nuna takardar naɗinsa ko wata shaida ta takarda da ke nuna cewa gwamnati ta ɗauke shi aiki, sannan ya ƙi amsa ƙarin tambayoyi, yana mai cewa lauyoyinsa sun shawarce shi da kada ya yi magana da 'yan jarida a halin yanzu.
"Na yanke shawarar yi muku magana ne kawai saboda girmamawa. Lauyoyina suna aiki a kan wani abu. Duk abin da suka ce, zan sanar da ku."
- Adeniyi Adeyemi
Ya ce rayuwarsa na cikin hatsari
Adeyemi ya yi ikirarin cewa rayuwarsa tana cikin haɗari, yana mai cewa hakan ya tilasta masa ɓoyewa.
"Yanzu suna neman rayuwata. Na tafi ɓuya. An daina jin motsina."
- Adeniyi Adeyemi
Lokacin da aka matsa masa lamba a kan takamaiman inda yake da kuma ko ya tsere daga ƙasar, ya ce ba zai iya bayyana wannan bayanin ba.
"Ba zan iya bayyana wani bayani ba a yanzu. Ba na ɗaukar kaina a matsayin wanda ke cikin aminci."
- Adeniyi Adeyemi

Source: Facebook
Zarge-zargen gwamnati kan Adeyemi
Fadar shugaban ƙasa ta zargi Adeyemi da ƙirƙirar takardun bada aiki na gwamnati da sauran takardu, da kuma bayyana kansa a matsayin shugaban PFIPC da PEAC, hukumomin da ta ce ba su wanzu ba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce 'yan sanda sun gurfanar da Adeyemi da wasu mutane biyu da ake tuhuma a kan tuhume-tuhume guda takwas a babbar kotun tarayya.
Ya ce shari'ar, wadda aka shigar a ranar 27 ga Nuwamba, 2025, an tsara za a saurare ta a ranar 27 ga Yulin 2026.
Amincewar gwamnati kan daukar ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bada damar daukar ma'aikata ga hukumar PFIPC da ake cece kuce a kanta.
Gwamnatin tarayya ta ba hukumar PFIPC da Adeniyi Adeyemi ke ikirarin shugabanta damar daukar ma'aikata guda 300 a watan Agustan shekarar 2025.
Adeyemi ya kuma nuna cewa hukumar ta samu amincewa na "kafa ofisoshin PFIPC a daukacin jihohi 36 na tarayya" da kuma "bude ofisoshi 127 a fadin duniya".
Asali: Legit.ng

