Zargin Batan Ƙoda: Iyalan Matar Aure Sun Nemi Gwamnatin Gombe Ta Bi Masu Hakki

Zargin Batan Ƙoda: Iyalan Matar Aure Sun Nemi Gwamnatin Gombe Ta Bi Masu Hakki

  • Ana zargin Asibitin Kwararru na jihar Gombe da cire wa Barira Alhassan ƙoda yayin tiyatar haihuwa
  • Iyalan Barira sun ce tsofaffin bayanan lafiyarta sun nuna tana da ƙododi biyu, saboda haka suka nemi bincike mai zaman kansa
  • Asibitin ya ce binciken likitoci ya nuna babu cire ƙoda yayin tiyata, yayin da iyalin ke jiran sakamakon cikakken bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Wata mata a Gombe, Barira Alhassan mai shekara 38 kuma uwa mai 'ya'ya 10 ta zargi Asibitin Kwararru na Gombe da cire mata ƙoda.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tana zargin an cire mata koda ɗaya yayin tiyatar haihuwa ta ake kira 'cesarean'.

Ana zargin an sace kodar mata a asibitin Gombe
Babbar mashigar Asibitin kwararru na jihar Gombe. Hoto: Yusuf Alyusra.
Source: Facebook

Zargin ya jawo hankalin jama'a, yayin da iyalanta suka nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano abin da ya faru, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Yadda Barira ta kwanta a asibitin kwararru a Gombe

Barira ta ce an kwantar da ita a asibiti ranar 8 ga Afrilu, 2026 bayan ta samu matsala yayin nakuda.

Ta ce likitoci sun sanar da iyalanta cewa ba za ta iya haihuwa ta hanyar al'ada ba, saboda haka aka ba da shawarar a yi mata tiyatar gaggawa, ta ce an yi aikin cikin nasara kuma ta haifi jariri lafiya.

Sai dai bayan an sallame ta daga asibiti, ta ce lafiyarta ta fara tabarbarewa. Ta ce ta fara amai, ciwon ciki, kumburin jiki da kuma tsananin ciwo yayin fitsari.

Barira ta ce tun farko ta yi tunanin matsalolin na daga cikin abubuwan da ke biyo bayan tiyatar haihuwa, amma daga baya ta damu saboda rashin samun sauƙi.

Ta ce ta tambayi wasu mata da aka yi wa irin wannan tiyata ko sun fuskanci irin waɗannan matsaloli, amma mafi yawansu sun ce ba su taɓa fuskantar haka ba.

Daga baya ta ce an yi mata ƙarin gwaje-gwaje, inda wani likita ya sanar da ita cewa tana da ƙoda guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar Gbajabiamila: Jam'iyyar NDC ta mika bukata ga Tinubu da EFCC

Yayan Barira, Zakariyya Alhassan, ya ce iyalansu sun fara nuna damuwa bayan sun kwatanta tsoffin bayanan lafiyarta da sabbin sakamakon gwaje-gwaje.

Ya ce binciken da aka yi mata a shekarar 2015 ya nuna tana da ƙododi biyu masu lafiya, amma bayan tiyatar haihuwar ne aka gano tana da guda ɗaya.

Zakariyya ya ce daga baya suka kai ƙorafi ga Ma'aikatar Lafiya ta jihar Gombe, wacce ta gayyaci bangarorin biyu tare da ba su shawarar kada su yi magana a bainar jama'a kafin a kammala bincike.

An bukaci gwamnati ta yi bincike kan batar koda a asibtin Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe. Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya.
Source: Facebook

Abin da mijin Barira ya ce

Mijin Barira, Malam Babayo Muhammad wanda aka fi sani da Auwalu Mai Lemo Pantami, ya ce matarsa ta haifi dukkan 'ya'yanta tara da suka gabata ba tare da tiyata ba.

Ya ce wannan ciki shi ne na goma, kuma likitoci sun bayyana cewa ta samu matsala yayin nakuda, lamarin da ya sa suka ba da shawarar tiyatar cesarean.

Har ila yau, ya ce likitocin sun kuma ba da shawarar a ɗaure mahaifarta domin kauce wa sake samun ciki saboda yanayin haihuwar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Minista ka iya rasa kujerarsa, an kirayi Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci

Babayo ya ce iyalansu sun amince da hakan tare da sanya hannu kan takardun amincewa kafin a fara aikin tiyatar.

Ya ce bayan an fito da ita ba ta da ƙarfi kuma ba ta amsawa yadda ya kamata, sai daga baya wani likita ya kula da ita ta farfaɗo.

Bayan sun koma gida, ya ce ta ci gaba da fama da kumburi, rauni, yawan fitsari da kuma wahalar tafiya.

Ya ce sun sake komawa asibiti inda aka tura ta yin hoton ciki, kuma wanda ya yi gwajin ya ce ƙoda guda ɗaya kawai ake gani.

Babayo ya ce wani likita ma ya tambayi matarsa ko ta taɓa sayar da ƙodarta bayan sakamakon gwajin ya nuna tana da guda ɗaya.

A cewarsa, Daraktan Lafiya na asibitin ya bayyana cewa wurin da ake yin tiyatar 'cesarean' ya bambanta da inda ƙoda take, saboda haka cire ƙoda yayin irin wannan tiyata ba abu ne mai yiwuwa ba.

Babayo ya ce daga baya lafiyar matarsa ta ƙara tabarbarewa, inda aka kwantar da ita a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe domin ci gaba da jinya.

Kara karanta wannan

DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

Ya roƙi gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da an gudanar da bincike cikin gaskiya domin tabbatar da adalci ga matarsa.

Martanin asibitin kwararru a Gombe

A nasa bangaren, Asibitin Kwararru na Gombe ya musanta zargin gaba ɗaya, yana mai cewa babu wata hujjar likitanci da ke nuna an cire wa Barira ƙoda.

Asibitin ya bayyana cewa bayanan ɗakin tiyata sun nuna an yi mata tiyatar cesarean ta gaggawa kawai, ba tare da wani aiki da ya shafi ƙoda ba.

Abin ke jawo ciwon koda

A baya, mun ba ku labarin cewa masana kiwon lafiya sun ja hankalin mutane game da illolin ciwon koda a jikin dan Adam.

Wasu mutane na alfahari kan yadda suke iya rike fitsari zuwa tsawon lokaci, kuma sai lokacin da ya ga dama suke yi wanda hakan illa ne ga koda.

Masana lafiya sun magantu kan irin wannan dabi'ar sannan kuma sun fadi illar da ahakn ke haifarwa In mutum bai yi wasa ba ya kan iya rasa rayuwarsa sabida rike fitsari ba tare da yayi shi akan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.