Sokoto: Jama'a Sun Shiga Firgici da 'Yan Bindiga Suka Kashe Limami da Wasu Mutane

Sokoto: Jama'a Sun Shiga Firgici da 'Yan Bindiga Suka Kashe Limami da Wasu Mutane

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan harin ta'addanci a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Hatsabiban sun hallaka limami da wasu mutane uku tare da yin garkuwa da wasu daban zuwa cikin daji a yayin harin
  • Mutanen yankin sun koka da cewa harin ya jefa su cikin tsaro da fargaba inda da dama daga cikinsu suke shirin daina kwana a garin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Miyagu da ake zargi 'yan bindiga ne sun kashe wani Limami da wasu mutane uku a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutane 12 a wani hari da suka kai ƙauyen Illelar Dawagware da ke yankin karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun yi kisa a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun afkawa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 12:20 na dare a ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026 inda suka zo a kan babura kusan guda tara.

Kara karanta wannan

Duk da tatsar N10m daga ƴan yankin, ƴan bindiga sun kona makaranta kurmus

'Yan bindiga sun yi ta'addanci a Sokoto

Maharan, waɗanda aka ƙiyasta yawansu ya kai kusan mutane 30, an bayyana cewa sun shafe kusan mintuna 30 suna cin karensu ba babbaka, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa.

Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana cikin sharadin sakaya sunansa, ya ce mutanen ƙauyen sun yi ƙoƙarin korar maharan amma makamansu sun fi ƙarfin na su.

A cewarsa, 'yan bindigan sun afka gidan limamin ƙauyen ne, inda suka kashe shi da wasu mutane uku, kafin su riƙa bi gida-gida suna yin garkuwa da mutane har 12.

“Sun kashe limaminmu, maƙwabcinsa da kuma wani mutum ɗaya. Daga baya suka yi garkuwa da mutane 12, waɗanda suka haɗa da mata takwas da maza huɗu." In ji shi

Ya ƙara da cewa daya daga cikin waɗanda aka kashe (Awwalu), 'yan bindigan sun kuma yi garkuwa da matarsa da ƙannensa guda biyu na jini a cikin gida ɗaya.

An kashe mutane yayin harin

Kara karanta wannan

'Yaran jagoran 'yan bindigan da suka sace Janar sun sake sabon ta'addanci a Katsina

An gano sunayen mamatan da aka kashe da cewa su ne Mallam Liman Lawwali Na Ande, Lawwali Na Lami, da kuma Abdullahi Haruna.

Waɗanda 'yan bindigan suka yi garkuwa da su sun haɗa da Amiru, Hauwa, Awwalu da sauran mutane tara.

Majiyar ta ƙara da cewa Alhaji Samaila ya samu raunin harbin bindiga wanda ya karya masa hannu, kuma a halin da ake ciki yana karɓar magani a wata cibiyar kiwon lafiya a Sokoto.

Mazauna yankin sun kuma zargi jami'an tsaro da gaza kawo agajin gaggawa lokacin da aka kira su a yayin da ake kai harin.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane sun shiga firgici

Wani mazaunin garin na daban wanda ya halarci jana'izar limamin ya ce tsoro ya mamaye al'ummar garin, inda ya ƙara da cewa mazauna ƙauyen da dama sun yanke shawarar ba za su sake kwana a ƙauyen ba.

“Yanzu za su riƙa kwana ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Goronyo saboda suna fargabar sake fuskantar wani harin." In ji shi

'Yan bindiga sun kona makaranta

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun ƙona wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Borgu ta Niger.

Kara karanta wannan

An kama mota cike da takalma irin na sojoji ta nufi dajin Zamfara

Hatsabiban 'yan bindigan sun ɗauki wannan matakin ne duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa ƙauyuka da al’ummomin gundumar Dekara sun haɗa kuɗi tare domin biyan Naira miliyan 10 da 'yan bindigar suka nema bayan sun yi barazanar kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng