'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

- Rahotanni sun bayyana cewa, an yi awon gaba da mutane da dama a wani hari a jihar Neja

- An kuma ji wa wasu raunuka yayin da 'yan bindigan ke yin awon gaba da shanun mutane

- Wata kungiya a jihar ta bayyana al'ummar yankunan ke fama da rashin tsaro a kauyukansu

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da mutane 35 tare da jikkata wani guda yayin da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da shanu da ba a san adadinsu ba yayin wani hari a Chiri Boda da Fuka da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Harin na baya-bayan nan, a cewar majiyoyi daga yankin, ya faru ne a jiya Asabar 24 ga watan Afrilu, Daily Trust ta ruwaito.

Yawancin mazauna kauyukan sun tsere zuwa daji don tsira da rayukansu.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja
'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban kungiyar Niger Concern Citizens, Alh. Muhammad Awaisu Wana, ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna babban birnin jihar.

Wana, wanda ya bayyana yadda mazauna yankin ke cikin tsananin damuwa da takaici, ya koka kan yadda a yanzu gundumomi goma cikin goma sha biyar a karamar hukumar Shiroro ke karkashin ikon 'yan bindiga.

Ya ce, "Unguwanni biyar da ba sa karkashin ikon 'yan ta'adda su ne Gusoro Zumba, Bongajiya, Bina, Sheyi lapa da Ubandoma kuma galibi sun cika ne da 'Yan Gudun Hijira (IDPs) daga sassa daban-daban da ke neman mafaka.

Ya kuma ce takwas daga cikin sassan da ke karkashin ikon 'yan bindigan suna cikin yankunan kogi.

Don haka, ya roki gwamnatin tarayya da ta kawo musu agaji cikin gaggawa domin basu damar komawa gida da kuma fara shirye-shiryen noman daminar bana.

Wana, wanda ya bayyana cewa 'yan gudun hijirar a cikin karamar hukumar sun fi 80,000 a yanzu, ya ce akwai bukatar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta wadata wadannan 'yan gudun hijirar da tallafin da ya kamata don magance matsalolinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DPS Wasiu Abiodun, lokacin da aka tuntube shi ya ce sai daga baya zai tuntubi manema labarai.

KU KARANTA: Buhari ya girgiza: Mutuwar Deby ta haifar da ‘Babban Gurbi’ a yaki da Boko Haram

A wani labarin, Kungiyar 'Yan Asalin Biyafara (IPOB) ta yi Allah wadai da kisan mambobinta a jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Sojojin Najeriya sun ce jami'an tsaro sun kai samame a hedikwatar kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) da ke jihar a ranar Asabar.

Mataimakin kwamandan kungiyar, wanda aka bayyana a matsayin kwamanda Ikonson da wasu mambobi shida sun mutu a yayin samamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel