Najeriya Ta Samu Daukaka, An ba Ta Kujera a Hukumar IEA ta Duniya
- Najeriya ta samu nasarar zama mamba a Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA), lamarin da ake ganin zai bunkasa zuba jari da samar da wutar lantarki
- Hukumar IEA ta bayyana cewa shigar Najeriya zai karfafa tsarin tafiyar da harkokin makamashi a duniya
- Najeriya ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta shiga IEA, wadda ke hada kasashe masu samar da makamashi da masu amfani da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da harkokin Gas, Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo, ya sanar da cewa Najeriya ta zama mamba a hukumar makamashi ta duniya (IEA).
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Ekpo ya ce an amince da Najeriya a matsayin mamba mai matsayin 'Association' a Hukumar IEA.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa ministan ya bayyana matakin a matsayin babban ci gaba ga kokarin Najeriya na fadada samun makamashi, bunkasa masana'antu da kuma samar da makamashi mai dorewa.
Amfanin shiga IEA ga Najeriya
Ekpo ya ce amincewar da Kwamitin Gudanarwar IEA ya yi baki daya na nuna irin muhimmanci da ɗaukakar da Najeriya ke kara samu a harkokin makamashi a duniya.
Ya ce wannan hadin gwiwa zai ba Najeriya damar cin gajiyar kwarewa, bincike, zuba jari da shawarwarin manufofi domin bunkasa fannin gas, samar da wutar lantarki da kuma hanyoyin samar da makamashi mai dorewa.
Ya ce:
"Na yi matukar farin ciki da yadda kasashe mambobin IEA suka karbi Najeriya a matsayin mamba. Babban abin alfahari ne gare mu mu shiga wannan hukuma ta duniya."
Ya kuma bukaci sauran kasashen Afirka su kara hada kai da IEA domin cimma burin samar da makamashi ga kowa da kuma bunkasa masana'antu.
Abubuwan da Najeriya za ta amfana
Ministan ya ce wannan mataki zai ba Najeriya damar samun karin ilimi da bincike kan harkokin makamashi, tare da karfafa hadin gwiwa a fannoni kamar, tsaron makamashi, jawo masu zuba jari, bunkasa fannin gas da fadada samar da wutar lantarki.

Kara karanta wannan
An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi
Ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen gina bangaren makamashi mai karfi da gasa a Najeriya, kamar yadda Guardian ta rahoto.
Hukumar IEA ta yabawa Najeriya
Najeriya ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta shiga shirin Association na IEA, wanda ke hada manyan kasashe masu samar da makamashi da masu amfani da shi domin tabbatar da samar da makamashi mai inganci, araha da dorewa.

Source: Twitter
Daraktan Janar na IEA, Fatih Birol, ya bayyana shigar Najeriya a matsayin muhimmin ci gaba ga hukumar da kuma al'ummar duniya baki daya.
Ya ce:
"Na yi matukar farin ciki da shigar Najeriya cikin IEA. Ita ce kasa mafi yawan al'umma a Afirka kuma babbar kasa ce a harkokin makamashi. Wannan mataki babban ci gaba ne ga tsarin tafiyar da harkokin makamashi a duniya."
Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Minista Ekpo bisa amincewar da suka nuna wa hukumar.
Tinubu zai biya bashin wutar lantarki
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya daukar mataki mai muhimmacin a bangaren wutar lantarki domin inganta fannin makamashi a Najeriya.
Tinubu ya umarci kwamitin shugaban Ƙasa kan harkokin wutar lantarki ya ware Naira tiriliyan huɗu domin biyan tsofaffin basussukan bangaren wutar lantarki a Najeriya.
Ya ce lokacin da gwamnatinsa ta karɓi mulki a shekarar 2023, bangaren wutar lantarki ya kasance cikin matsalolin ƙarancin samar da wuta.
Asali: Legit.ng

