Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garin rogo

Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garin rogo

  • Yan sanda a Delta sun yi nasarar kama wani mutum da harsashin AK-47 guda 340
  • 'Yan sandan sun gano harsahin ne cikin buhun garrin rogo da mutumin ya boye
  • Har wa yau, yan sandan sun kuma yi nasarar wata mata da double-barrel da harsashi 26

Delta - Yan sanda a jihar Delta sun kama wani Solomon Ebe kan mallakar harsashi masu rai na AK-47 da aka boye cikin buhun garrin rogo, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Bright Edafe ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Warri.

Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo
Hoton mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo a Delta. Hoto: 9ja Breed
Source: Facebook

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Mr Edafe ya bayyana cewa yan sandan yankin Bomadi ne suka kama wanda ake zargin ne a ranar Juma'a yayin da suke tsare ababen hawa suna bincike a cewar rahoton na Premium Times.

Ya ce yan sandan sun fita suna tare ababen hawa ne kuma suna bincike a Bomadi/Tuoma a karamar hukumar Bomadi na jihar yayin da suke yi kamen.

Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo
A dai-daita sahun da aka kama mutumin a ciki. Hoto: 9ja Breed
Source: Facebook

Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo
Hoton mutumin da aka kama da harsashin AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo a Delta. Hoto: 9ja Breed
Source: Facebook

Ya ce:

"A ranar 1 ga watan Oktoban 2021 misalin karfe 07:30hrs, yan sanda na yankin Bomadi yayin tare ababen hawa da bincike a Bomadi/Tuomo sun kama wani mai adaidaita dauke da wani Ebe wanda ya dako buhun garin rogo.
"Yan sandan sun yi zargin akwai lauje cikin nadi don haka suka yanke shawarar bincikar wanda ake zargin da buhun.
"Yayin binciken, sun gano harsashin AK-47 340 masu rai da aka boye cikin garrin, an damke wanda ake zargin kuma ana fadada bincike."

Read also

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

An kuma kama wata da double-barrel da harsashi 26

Kazalika, yan sandan sun kama wata Ejiro Efemijoghor da ake zargi da mallakar bindiga double-barrel da harsashi guda 26.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba a yayin da yan sandan Raider Squad ke bincike.

Hotunan mutumin da aka kama da harsashin bindiga ƙirar AK-47 guda 340 a cikin garrin rogo
Hoton bindiga da harsashi da aka kama hannun wata mata Efemijoghor a Delta. Hoto: 9ja Breed
Source: Facebook

Da aka mata tambayoyi, Efemijoghor ta ce bindigan da harsashin na mijin ta ne.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Source: Legit

Online view pixel