'Yan Kwallo Sun Rasu bayan Hadari a Kebbi, Gwamna Ya ba Su Miliyoyin Naira
- Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan wasan ƙwallo sun mutu a hadarin mota da ya rutsa da su a Birnin Kebbi a kan hanyar wasan sada zumunta
- Gwamna jihar Kebbi, Nasir Idris ya halarci aikin ceto matasan d akan shi bayan ya shaida hadarin da idanunsa, tare ba da umarnin tallafa masu
- Gwamnatin jihar Kebbi ta ba iyalan wadanda suka rasu kudi har Naira miliyan 20, tare da ba da tallafi ga sauran da suka jikkata a cikin motar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi - Matasa biyar da ke tafiya daga yankin Ambursa na Birnin Kebbi domin buga wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci sun rasu sakamakon hadarin mota da ya faru a kan titin Filin Jirgin Sama da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.
Hadarin ya faru ne bayan wata motar Toyota Sienna da ke ɗauke da mutum 18 ta ƙwace wa direba sannan dungura a kan titi yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wasan.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa gwamnatin jihar ta ba iyalan wadanda abin ya shafa tallafin kudi domin rage radidin halin da suka shiga.
Bayanin gwamnan Kebbi
Yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai fadar hakimin Ambursa a madadin Gwamna Nasir Idris, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Abubakar Umar Dutsinmari, ya bayyana cewa gwamnan ya shaida hadarin da idanunsa.
Kwamishinan ya ce Gwamna Idris ya bayar da umarnin ɗaukar matakan gaggawa domin ceto rayukan waɗanda suka jikkata a hadarin.
Dutsinmari ya bayyana mutuwar matasan biyar a matsayin babban rashi, ba ga al'ummar Ambursa kaɗai ba, har ma da daukacin jihar Kebbi.
Ya tabbatar wa iyalan mamatan da waɗanda suka jikkata cewa gwamnan zai ci gaba da nuna alhini da kuma ba su cikakken goyon baya.

Source: Original
Gwamnan ya ba da tallafin N20m
A madadin gwamnan jihar, Dutsinmari ya miƙa tallafin Naira miliyan 20 ga iyalan mamatan, Naira miliyan 1 ga kowane mutum da ya jikkata, sannan naira miliyan 2 ga sauran fasinjojin motar.

Kara karanta wannan
Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi
Da yake mayar da martani, Hakimin Ambursa, Alhaji Isah Haruna Rasheed, ya nuna matuƙar godiyarsa ga Gwamna Nasir Idris bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tallafin kuɗi da ya bai wa waɗanda hadarin ya shafa.
The Sun ta rahoto ya ce:
“Gwamnan ya yi abin da ake tsammani daga gare shi ta hanyar turo tawaga mai ƙarfi da ta ƙunshi kwamishinoni uku da masu ba shi shawara na musamman da dama domin yi mana jaje.
“Mun yi matuƙar jin daɗi da ganin cewa da ya isa wurin hatsarin, gwamnan ya tsaya ya kuma taimaka da kansa wajen kwashe gawarwakin.
An sa wa manoma haraji a Kebbi
A wani rahoton, kun ji cewa shgabannin wasu al'ummomi a jihar Kebbi sun sanar da cewa wasu 'yan ta'adda sun kakaba masu haraji.
Mutanen sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun sanya masu harajin kudi har Naira miliyan 6 kafin su samu damar yin noma a damunar bana.
Mutanen yankin da aka kakabawa harajin sun bayyana cewa suna cikin damuwa, inda suka fara neman agaji daga hukumomin tsaro.
Asali: Legit.ng
