"Ka da Ku Bata Kuri'unku"; Sanata Kalu Ya Bayyana Abokin Hamayyar Tinubu a 2027

"Ka da Ku Bata Kuri'unku"; Sanata Kalu Ya Bayyana Abokin Hamayyar Tinubu a 2027

  • Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, Sanata Uzor Orji Kalu, ya tabo batun tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Uzor Orji Kalu ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai da abokin hamayya a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya bukaci mutanen yankinsa kan kada su bata kuri'unsu a lokacin babban zaben da ake tunkara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Abia - Sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da wani dan takara mai karfi da zai fafata da shi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kalu ya yi magana kan Shugaba Tinubu
Sanata Uzor Orji Kalu da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Uzor Orji Kalu, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce Kalu ya fadi hakan ne ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026 yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar Abia da aka gudanar a Umuahia.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Sanata Orji Kalu ya tattauna kan batutuwan da suka shafi hadin kan jam'iyyar APC a jihar Abia, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Me Kalu ya ce kan zaben 2027?

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce jam'iyyar APC mai mulki za ta rike mulki saboda jam'iyyun hamayya sun yi rauni da ba za su iya nuna wani kalubale na azo a gani ba.

Ya bayyana cewa Tinubu ne har yanzu dan takara mafi karfi a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

"Labari mai dadi shi ne za mu lashe zaben kasar nan cikin sauki. Shugaba Tinubu ba shi da abokin takara, ba shi da mai kalubalantarsa. Jam'iyyun hamayya sun wargaje, sun ruguje baki daya, ku nakalto maganata."
"Wataƙila idan Orji Kalu ne ke takara a APC, hakan zai iya zama kalubale ga Shugaba Tinubu. Amma a yau babu wani kalubale, saboda ba za ka iya amfani da yankin Kudu-maso-Gabas kadai ko wani wuri daban don kalubalantar shugaban kasar Najeriya ba."
"Wannan ba zai yiwu ba. Kar mu zubar da kuri'unmu. Mu bari kuri'unmu su kasance masu tasiri."

Kara karanta wannan

"Ni ba ungulu ba ne:" Ganduje ya yi martani ga zargin zai hade da Kwankwaso

- Sanata Orji Kalu

Sanata Kalu ya yi magana kan zaben 2027
Sanata Uzor Orji Kalu a zauren majalisar dattawa Hoto: Uzor Orji Kalu
Source: Facebook

Kalu ya yi maganar siyasa a Najeriya

Dan majalisar, wanda ya bayyana kansa a matsayin "masanin kimiyyar siyasa" kuma dan kasuwa, ya ce wannan bincike nasa ya dogara ne a kan fahimtarsa game da yanayin siyasar kasar.

Ya bayyana cewa lissafin zabe na Najeriya ya sa ba zai yiwu wani dan takara ya zama shugaban kasa ba tare da samun gagarumin goyon baya daga sassan kasar baki daya, inda ya bukaci al'ummar Igbo da su yi aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kan kasa idan suna fatan samar da shugaban kasa a nan gaba.

NDC ta soki Sanata Kalu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya ta soki Sanata Uzor Orji Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa.

Jam’iyyar NDC ta soki Orji Uzor Kalu, kan kalaman da ya yi na yabon gyaran tattalin arzikin shugaba Bola Tinubu.

NDC mai adawa ta ce kalaman babban mai tsawatarwar na Majalisar Dattawa na yaudara ne kuma ba su dace da halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba na wahalhalun rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng