Trump Ya Lallaba Ya Tura Bukatar Tsagaita Wuta Iran ta Iraq, Tehran Ta Yi Martani
- Iran ta ƙi amincewa da wata sabuwar shawarar tsagaita wuta da Amurka ta aike mata ta hannun Firaministan Iraki, Ali al-Zaidi
- Rahotanni sun nuna cewa Tehran ta ce shawarwarin ba su magance rikicin da ya shafi ikon sarrafa mashigar ruwa ta Hormuz ba
- Yayin da rikice-rikice da yaki ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya, sojojin Amurka sun kai hare-hare kan Iran na dare na 13 a jere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran – Gwamnatin Iran ta yi watsi da wata shawarar tsagaita wuta da Amurka ta gabatar mata ta hannun Firaministan Iraki, Ali al-Zaidi, yayin da rikicin tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da tsananta.
Rahotanni sun bayyana cewa Firaministan Iraki ya kai wannan saƙo ne lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a hukumance zuwa Tehran tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2026.

Source: Getty Images
New York Times ta ce Ali al-Zaidi ya kai ziyarar ne bayan ya gana da Shugaban Amurka, Donald Trump, a Fadar White House, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi rikicin da ke tsakanin Washington da Tehran.
Dalilin da Iran ta ƙi tayin Amurka
Rahotanni da suka ambato jami'an Iran da na Iraki sun ce gwamnatin Tehran ta yi watsi da tayin ne saboda ba ya ƙunshe da mafita kan batun ikon sarrafa mashigar ruwa ta Hormuz.
Mashigar Hormuz na daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar ɗanyen mai, kuma Iran ta dade tana kallon batun a matsayin muhimmin ɓangare na tsaronta da tattalin arzikinta.
Sai dai Anadolu Agency ta wallafa cewa gwamnatin Iran ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da rahoton ba.
Abubuwan da aka tattauna a Iran
A yayin ziyarar, Firaministan Iraki ya gana da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, inda suka tattauna dangantakar ƙasashen biyu da kuma hanyoyin ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a yankin.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka rattaba hannu a baya, tare da faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin kasuwanci, makamashi, sufuri da sauran harkokin yanki.
Haka kuma, kafofin yaɗa labaran Iran sun ce Ali al-Zaidi ya gana da shugaban Majalisar Dokoki, Mohammad Bagher Ghalibaf, da Ministan Harkokin Waje, Abbas Araghchi.

Source: Getty Images
A gefe guda, rundunar Amurka ta CENTCOM ta sanar da cewa dakarunta sun kai hare-hare kan wurare a Iran na dare na 13 a jere.
A cewar rahoton, wasu jami'an Iran sun shaida cewa idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare, Tehran za ta faɗaɗa rikicin zuwa wasu yankuna.
Isra'ila ta kai hare-hare a Gaza
A wani labarin, mun ruwaito cewa Isra'ila ta ba mazauna wasu yankuna na Gaza umarnin ficewa kafin daga bisani ta kai hare-haren sama da suka yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa biyu.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun lalata gidaje a sansanonin 'yan gudun hijira da wasu unguwanni na birnin Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya.
Rahoto ya nuna cewa jami'an ceto sun ci gaba da kokarin kashe gobara bayan hare-haren, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsananciyar matsalar jin kai a yankin.
Asali: Legit.ng

