Yadda ake Farautar 'Yan Najeriya da Kasashe da Sanduna a Afrika Ta Kudu

Yadda ake Farautar 'Yan Najeriya da Kasashe da Sanduna a Afrika Ta Kudu

  • Tarin mutane na gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na Afirka ta Kudu a kan neman baƙin haure su fice daga kasar a gaggawa
  • A yanzu haka dubban baƙin haure sun fice daga yankunansu, yayin da wasu mutane suka mutu a zanga-zangar da ake yi a kasar
  • Wasu ƙasashen Afirka ciki har da Najeriya sun tura jirage da motoci domin dauko 'yan ƙasarsu saboda tsoron kar a kai masu hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

South Africa - Duddab 'yan Afrika ta Kudu sun gudanar da zanga-zanga a ranar Talata a birane daban-daban na kasar domin neman dukkan baƙin hauren da ba su da takardun izinin zama su bar ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan wani gangamin da ya ɗauki makonni da ya tilasta wa dubban mutane tserewa tare da yin sanadin mutuwar mutum huɗu.

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Yadda ake zanga-zangar Afrika ta Kudu
Wasu masu zanga-zanga a Afrika ta Kudu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta wallafa cewa masu zanga zangar sun sanya ranar 30 ga Yunin 2026 a matsayin wa'adin da baƙin hauren da ba su da takardu za su fice daga ƙasar.

An yi satar kayayyaki

An samu rahotannin satar kayayyaki, jifan duwatsu da arangama a wasu wurare, ciki har da kusa da Johannesburg, inda jami'an tsaro suka raka wasu ƙalilan daga cikin baƙin hauren daga cikin wata taron masu zanga-zanga da ke riƙe da manyan sanduna.

Masu zanga-zangar sun yi jerin gwano a tsakiyar Johannesburg, cibiyar harkokin kuɗi ta Afirka ta Kudu, inda yawancin shaguna suka kasance a rufe, ma'aikata suka zauna a gidajensu, sannan tashoshin sufuri suka yi tsit.

Sun riƙe tutoci da alluna dauke da rubuce-rubuce yayin da 'yan sanda sanye da rigunan kariya da hular yaƙi suke sa ido a wurare.

A birnin Durban da ke kudu maso gabashin ƙasar, wanda ake kallon cibiyar al'ummar Zulu, masu zanga-zangar sun fito cikin kayan gargajiyar mayaƙa, suna ɗauke da mashi, bulala da garkuwa, yayin da wasu suka yafa fatar damisa.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi magana kan kashe malamar Islamiyya a Kaduna

'Muna son a kori su gaba ɗaya'

Ƙungiyoyin da ke yaƙi da baƙin haure ba tare da takardu ba suna zargin cewa suna ƙwace wa 'yan ƙasar ayyukan yi da ayyukan gwamnati, ikirarin da masana ke cewa baƙin haure ne ake ɗora wa laifin gazawar gwamnati.

Jagorar ƙungiyar March and March mai adawa da baƙin haure, Jacinta Ngobese-Zuma, ta shaida wa masu zanga-zanga a Durban cewa:

“Baƙin hauren da ba su da takardu sun maye gurbin 'yan Afirka ta Kudu, lamarin da ya ƙara rashin aikin yi.”

Ta ƙara da cewa

“Muna son a kori su gaba ɗaya. A cikin watanni shida masu zuwa muna son gwamnati ta kawar da duk waɗanda ba su fice ba.”

Ga bidiyon masu zanga-zangar a kasa:

Ana dauko 'yan Najeriya

Ƙasashen Afirka da dama, ciki har da Najeriya, Malawi, Ghana, Zimbabwe da Mozambique, sun shirya jiragen sama da motocin bas domin bai wa 'yan ƙasarsu damar komawa gida da son rai.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Hukumomi sun ce sama da mutum 25,000 aka kammala shirye-shiryen tafiyarsu daga ƙasar a cikin makonnin da suka gabata.

Kamfanin jirgin Air Peace ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya dauko wasu 'yan Najeriya da barazanar masu zanga-zanga suka sanya su dawowa gida.

Yan Najeriya daga Afrika ta Kudu
'Yan Najeriya da suka isa Legas daga Afrika ta Kudu. Hoto: Air Peace
Source: Facebook

Najeriya ta nemi agajin kasashe

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa tana cigaba da neman hadin kan kasashe a yaki da rashin tsaro.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka, Donald Trump ke cewa ya kammala maganin 'yan ta'adda da ke kashe Kiristoci.

Najeriya ta bayyana cewa akwai bukatar hada kai tsakanin kasashe domin magance matsalar tsaro da ta addabi yankuna da dama na kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng