Fusatattun Dalibai Sun Rufe Kofa, Sun Hana Shugaban Jami'a Shiga cikin Makaranta

Fusatattun Dalibai Sun Rufe Kofa, Sun Hana Shugaban Jami'a Shiga cikin Makaranta

  • Daliban jami’ar fasaha ta tarayya Minna sun gudanar da zanga-zanga tare da rufe kofar jami’ar kan matsalar tsaro a wajen makaranta
  • Daliban sun ce hare-haren ‘yan fashi sun yi yawa a wajen makarantar, inda suka rasa kayayyaki tare da jikkatar wasu daga cikinsu
  • Mahukuntan jami’ar sun ce suna tattaunawa da ‘yan sanda da jami’an sa-kai domin ganin an inganta tsaro a yankunan wajen makarantar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Neja – Daliban jJami’ar fasaha ta tarayya Minna (FUT, Minna) sun toshe kofar jami’ar ranar Talata yayin wata zanga-zanga kan zargin yawaitar hare-haren 'yan fashi a wuraren da suke zaune a wajen makarantar.

Zanga-zangar ta kawo tsaiko ga harkokin karatu a jami’ar, inda daliban suka fara tare hanyar Minna zuwa Bida tun da misalin karfe 8:00 na safe, lamarin da ya sa matafiya suka kasa wucewa.

Kara karanta wannan

APC ta taɓa sunaye kafin mika wa INEC jerin ‘yan takara a zaben 2027

Dalibai sun gudanar da zanga zanga a jami'ar FUT Minna
Dandazon dalibai sun rufe babbar kofar shiga jami'ar FUT da ke Minna. Hoto: UGC
Source: UGC

Dalibai sun ki sauraron shugaban jami'a

Daga baya daliban sun koma babbar kofar shiga jami’ar domin nuna bacin ransu, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban jami’ar ya isa wurin domin kwantar da hankalin daliban, amma daliban suka ki sauraronsa

An ce daliban sun bukace shi da ya bar wurin, kafin jami’an tsaron jami’ar su samar da hanya domin ya shiga cikin makarantar.

Daliban sun hana wasu manyan jami’an jami’ar da suka hada da mataimakan shugaban jami’a, shugabannin bangarori da malaman jami’a shiga harabar.

An dakatar da jarrabawar zangon karatu

Daily Trust ta ruwaito cewa jami’ar na shirin fara jarrabawar kwamfuta ga daliban matakin 100 da 300, amma zanga-zangar ta hana gudanar da shirin.

Wani dalibi da bai bayyana sunansa ba ya ce daliban sun fusata ne saboda matsalar tsaro da suke fuskanta a wajen jami’ar.

Dalibin ya ce an kashe wani dalibi a harin fashi kwanaki uku da suka gabata, yayin da wani harin da aka kai daren da ya gabata ya jikkata wasu dalibai.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya aika sakon gaggawa ga gwamnati kan daliban da aka sace a Borno

Ya ce:

“Tsawon mako guda yanzu ba mu samu kwanciyar hankali ba saboda yawan hare-haren 'yan fashi. Muna ci gaba da rasa kayayyakinmu ciki har da kwamfutoci da wayoyi.
“Wasu daga cikin abokanmu sun samu raunuka a daren jiya. Shin za mu ci gaba da rayuwa haka? Gaskiya ba mu da lafiya.”
An zargi jami'ar FUT Minna da gaza daukar matakai yayin da dalibai ke fuskantar hare-haren 'yan fashi
Taswirar jihar Niger inda dalibai suka rufe kofar shiga jami'ar FUT. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An zargi jami’a da rashin daukar mataki

Dalibin ya zargi cewa sun sha kai rahoto ga mahukuntan jami’ar kan matsalar, amma ba a dauki wani mataki da zai kare su ba.

Wani ma’aikacin jami’ar da bai so a bayyana sunansa ba ya ce daliban sun kara fusata ne saboda kudin tsaro na N10,000 da suke biya a kowace zangon karatu.

Ya zargi mahukuntan jami’ar da rashin daukar matakan da suka dace domin magance matsalar tsaro a wajen harabar makaranta.

ASUU na barazanar tafiya yajin aiki

A wani labari, mun ruwaito cewa, ASUU ta soki gwamnatocin jihohi akalla bakwai kan rashin cika yarjejeniyar da aka cimmawa tsakaninta da gwamnatin tarayya a 2025.

Kara karanta wannan

Bayan kai hare hare, Amurka da Iran sun dauki sabuwar matsaya kan mashigar Hormuz

ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami'o'i 11 da ke wadannan jihohi matukar aka gaza biyan haƙƙokin malamai daga nan zuwa karshen watan Yuli.

Ta yi kira ga gwamnonin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar tare da biyan dukkan basussukan da ake bin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com