Tashin Hankali Yayin da Yan Sanda Suka Yi Arangama da Dalibai Masu Zanga-Zanga a Jami'ar ATBU

Tashin Hankali Yayin da Yan Sanda Suka Yi Arangama da Dalibai Masu Zanga-Zanga a Jami'ar ATBU

  • Harkokin karatu sun tsaya cak a harabar jami'ar ATBU da ke Yelwa bayan ɓarkewar zanga-zangar ɗalibai
  • Ɗaliban sun fito zanga-zangar ne bayan wasu mahara sun halaka wani ɗalibin ajin ƙarshe wajen ƙoƙarin sace masa waya
  • Sai dai, ɗaliban sun fuskance turjiya daga jami'an tsaro waɗanda suka harba musu barkonon tsohuwa domin hana su zanga-zanga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - An samu tashin hankali a harabar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Yelwa a Bauchi, yayin da ƴan sanda suka harbawa ɗaliban da suka fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa wani ɗalibi barkonon tsohuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu mahara ne da suke ƙoƙarin sace waya suka kashe wani ɗalibin ajin ƙarshe mai suna Joseph Agabaidu, har lahira.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sandan sun cafke gungun masu garkuwa da mutane a jihar Arewa

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a ATBU
Yan sanda sun kori daliban da ke zanga-zanga a ATBU Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Me nene ya haddasa zanga-zangar?

Ɗalibin mai karantar Geology wanda yake a 500L, an ce yana kan hanyar komawa gidansa da ke kusa da kasuwar Yelwan Tudu a unguwar Yelwa, a wajen birnin Bauchi, da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai masa hari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An garzaya da Agabaidu asibiti don duba lafiyarsa amma bai iya tsira da munanan raunukan da ya samu ba dalilin wuƙar da aka soka masa.

Ɗaliban sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar makarantar amma jami'an tsaro sun hana su.

Sun dage cewa sai sun fice zuwa wajen makarantar domin gudanar da zanga-zanga amma sai jami'an tsaro suka hana su.

An rufe ƙofar shiga jami'ar, inda jami’an ƴan sanda su yi baya da wajen amma suka ƙi. Daga nan ne ƴan sandan suka harba barkonon tsohuwa, lamarin da ya tilastawa daliban yin ƙaura daga bakin ƙofar.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe gawurtaccen ɗan bindigan da ya hana jama'a zaman lafiya a arewa

Ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa

Harba barkonon tsohuwan da ƴan sandan suka yi ya ƙara dagula lamura yayin da ɗaliban suka rufe ƙofar da karfi da yaji tare da toshe duk wata hanya a cikin harabar makarantar.

Hakan ya sa malamai da ɗalibai masu shiga da fita cikin makarantar suka yi cirko-cirko ayin da daliban suka ki bude kofa da barin zirga-zirgar ababen hawa da na mutane.

Har ila yau, harkokin karatu sun taɓu a harabar Yelwa da Gubi, saboda ɗaliban da ke shiga makarantar ba sa iya shiga, waɗanda ke zuwa harabar makarantar ta Gubi ma ba za su iya fita ba.

Ɗaliban UNICAL Sun Fito Zanga-Zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaliban jami'ar Calabar (UNICAL) sun fito zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makaranta.

Ɗaliban sun fito ne domin nuna adawarsu kan yadda mahukuntan makarantar suka ƙara kuɗin makaranta da kaso 100%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel