Daliban Najeriya Sun Fusata da Kama Aminu Muhammad, Za Su Yi Kwarya-Kwaryar Zanga-Zanga

Daliban Najeriya Sun Fusata da Kama Aminu Muhammad, Za Su Yi Kwarya-Kwaryar Zanga-Zanga

  • Kungiyar dalibai ta Najeriya (NANS) ta bayyana fushinta da yadda ake ci gaba da tsare dan uwansu dalibi kan zargin bata sunan Aisha Buhari
  • Kungiyar ta ce za ta ci gaba da yin zanga-zanga daga ranar 5 ga watan Disamba har sai an sako Aminu Muhammad da aka tsare
  • An tsare wani dalibi da ake zargin ya yiwa Aisha Buhari kalaman gatsali a kafar Twitter, hakan ya jawo cece-kuce

Shugabancin kungiyar dalibai ta Najeriya ta ayyana fara gangamin zanga-zanga a fadin kasar nan domin neman a sako dan uwansu dalibin jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, Aminu Muhammad da aka kama bisa zargin cin zarafin Aisha Buhari.

A makon nan ne rahotanni suka karade kasar nan na yadda aka kama wani matashi da ya yi rubutun gatsali ga uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafin Twitter.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari: Litinin Din Nan Mai Zuwa Dalbai Zasu Far Zanga-Zanga Dan A Saki Aminu

Shugaban kungiyar dalibai ta NANS, Usman Barambu ya fitar da sanarwa a ranar Alhamis, inda ya bayyana fara zanga-zangar dalibai a fadin kasar nan don nuna adawa da ci gaba da tsare Aminu.

Dalibai za su yi zanga-zanga kan kame Aminu Muhammad
Daliban Najeriya Sun Fusata da Kama Aminu Muhammad, Za Su Yi Kwarya-Kwaryar Zanga-Zanga | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Abu ya gagara, za mu dauki mata, inji daliban Najeriya

Bayan da hakan ya gagara, Usman Barambu ya fada a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa, ana cutar da Aminu, don haka ‘yan uwansa dalibai ba za su zauna suna ci gaba da jin labarin mummunan abinda ke faruwa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce za ta fito zanga-zanga a ranar 5 ga watan Disamba a fadin kasar nan don nuna koke da kuma rashin jin dadi da yadda aka cutar da Aminu.

Sanarwar ta ce, daliban za su ci gaba da zanga-zanga har sai an sako dan uwansu, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe, za a fara koyar da dalibai da harshen Hausa a makarantun firamare

Punch ta tattaro cewa, jami’an tsaro sun zo sun kama Aminu ne bayan da suka bi diddiginsa a jihar Jigawa tun daga babban birnin tarayya Abuja a watan Nuwamba.

Mai shari’a Halilu Yusuf na babbar kotun tarayya da zamanta a Abuja ya jiye Aminu a gidan gyaran hali na Suleja a jihar Neja bisa zargin bata sunan uwar gidan shugaban kasa.

Kama Adamu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda ‘yan Najeriya, ciki har da masu fada a ji ke nuna bacin ransu ga abin da ya faru tare da neman a sako dalibin.

Barambu ya ce NANS za ta ci gaba da zanga-zanga don nuna fushinta ga Aisha Buhari da kuma Sufeto Usman Alkali Baba.

A baya daliban Najeriya sun nemi afuwar Aisha Buhari, amma yanzu za su dauki mataki don nuna abin da aka yi bai dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel