Kano: An Gano Abin da Ya Jawo Mummunan Arangama tsakanin Manoma da Makiyaya
- An samu gagarumin sabani tsakanin wasu manoma da makiyaya a jihar Kano, lamarin da ya haddasa asarar dukiyoyi da jikkata bayin Allah
- Rikicin ya samo asali ne bayan saniya ta shiga gona ta lalata amfanin gona, lamarin da ya jawo martanin manoman da aka yi wa barna
- Tuni Shugaban ƙaramar hukumar da lamarin ya faru ya ba da umarnin a biya kuɗin jinyar waɗanda suka jikkata tare da yin kira ga zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Mutune aƙalla 12 ne suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Warawa da ke jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a gundumar Jigawa, inda rikicin ya shafi manoma daga ƙauyen Gadan Sarki da kuma makiyaya daga ƙauyukan Majawa da Karade.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza

Source: Original
Jaridar Daily Daily Trust ta wallafa cewa wani mazaunin yankin mai suna Balarabe Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa rikicin ya samo asali ne tsakanin mazauna ƙauyukan da abin ya shafa.
Yadda rikici ya balle a jihar Kano
Jaridar Daily Post ta kawo labarin cewa a cewarsa, Balarabe Ado ya bayyana cewa rikicin ya fara ne bayan wata saniya ta shiga gonar wani manomi ta ci amfanin gonarsa.
Ya ce manomin ya bugi saniyar saboda ɓarnar da ta yi, lamarin da ya sa mai ita ya rama ta hanyar dukan manomin, lamarin da ya jawo karin sabani.

Source: Facebook
A kalamansa:
"Rikicin ya fara ne lokacin da wata saniya ta shiga gonar wani manomi ta ci amfanin gonarsa. Sai manomin ya bugi saniyar, wanda hakan ya sa mai ita ya rama da dukan manomin."
"Nan take saɓanin ya rikide zuwa rikici mai faɗi, wanda ya yi sanadin jikkatar mutum 12."

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja
Kano: Shugaban karamar hukuma ya magantu
Shugaban ƙaramar hukumar Warawa a jihar Kano, Hon. Lamido Sunusi Ahmad, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Musleem Garindau, ya fitar.
Sanarwar ta ce shugaban ƙaramar hukumar ya kai ziyara Babban Asibitin Wudil domin duba waɗanda suka jikkata, inda ya ba da umarnin a biya duk kuɗaɗen jinyarsu har sai sun warke gaba ɗaya.
Ya yabawa shugabannin al'umma da jami'an tsaro bisa gaggawar da suka yi wajen shawo kan rikicin, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankin.
Lamido Sunusi Ahmad ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su guji yaɗa jita-jita ko aikata duk wani abu da ka iya ƙara ruruta rikicin.
An hukunta mai safarar makamai a Kano
A wani labarin kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yanke wa Raya Haruna hukuncin daurin shekaru 10 kan safarar makamai ga ‘yan bindiga da ke aikata ta'addanci a Arewacin kasar nan.
Alkalin kotun ya ce ko da ba ta shiga kai tsaye a hare-hare ba, rawar da ta taka ta taimaka wajen karfafa ayyukan ta’addanci, wanda ya zama babbar matsala ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
An kama matar ne a 2024 yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar domin dakile safarar makamai zuwa hannun ‘yan bindiga, sannan aka gurfanar da ita a gaban kotu bayan an shafe lokaci ana gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng
