Yadda Na Ke Kai Wa Yan Ta'adda Kayan Abinci Da Kudin Fansa A Zamfara - Wanda Ake Zargi

Yadda Na Ke Kai Wa Yan Ta'adda Kayan Abinci Da Kudin Fansa A Zamfara - Wanda Ake Zargi

  • Rundunar yan sanda a Jihar Zamfara sun yi nasarar kama wasu mutane da ake zargin suna kai wa yan bindiga makamai, kayan abinci da karbo kudin fansa
  • Alhassan Lawali, wani wanda ake zargin da aka kama ya amsa cewa ya dade yana kai wa yan bindiga babura a daji suna biyan shi kasonsa
  • Lawali ya ce yana sayarwa yan bindigan kowane babur kan N750,000 shi kuma suna bashi la'adar N15,000 sannan shine ke yi wa yan bindigan gyara idan babur dinsu ya lalace

Jihar Zamfara - Alhassan Lawali, wani da ake zargi dan leken asirin yan bindigan Zamfara ne ya bayyana yadda ya rika kai wa yan bindiga kudin fansa da kayan abinci.

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara, ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Wadanda ake zargi.
Yan Sanda Sun Kama Masu Kai Wa Yan Ta'adda Bindigu Da Kayan Sojoji A Zamfara. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Yayin amsa tambayoyi, wanda ake zargin (Lawali) ya amsa cewa ya kai wa yan bindigan babura fiye da 14 a daji kan N750,000 kowannensu, inda ya ke samun N15,000 kan kowane babur. Wanda ake zargin ya kara da cewa tsawon shekaru, shi ke gyara wa yan bindigan baburan.
"Wanda ake zargin, cikin sanarwarsa, kuma ya ambaci wani Mansur Usman a matsayin abokin harkallarsa, wanda shima daga baya yan sanda sun kama shi."

Da ake masa tambayoyi:

"Ya amsa cewa ya dade yana kai wa yan bindigan kayan abinci a daji. Ya kuma ce lokuta da dama, ya karbo wa yan bindigan kudin fansa. Kudin fansan na karshe da ya karbo shine N2.3m".

Yan sandan sun kuma kama wani wanda ake zargin, wanda ya yi ikirarin shi soja ne dauke da bindigan, kayan sojoji, katin shaida na karya da wasu makamai masu hatsari a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Bayyana Wa Yan Sanda Yadda Ya Ke Amfani Da Farin Takarda Wurin Damfara Masu POS

Ban San Adadin Mutanen Da Na Kashe Ba, In Ji Aliyu, Dan Shekara 24 Da Ake Zargi Da Fashi

A wani rahoton, an kama wani mai aikin gini, Adamu Aliyu, tare da wasu mutane hudu kan zargin fashi da makami da kisar gilla inda ya ce ba zai iya tuna adadin mutanen da ya kashe ba, rahoton The Punch.

Yan sanda sun yi holen Aliyu, wanda ke zaune a Ikire, Jihar Osun, da abokinsa, Yusuf Idris da wasu mutane uku a Osogbo kan zarginsu da hada baki da wasu wurin kashe wani manajan gidan man fetur, Fatai Adigun a Aku, garin Ikire.

Asali: Legit.ng

Online view pixel