Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Ba 'Yan Najeriya Muhimmiyar Shawara

Rashin Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Ba 'Yan Najeriya Muhimmiyar Shawara

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya buƙaci ƴan Najeriya da su rungumi ƙalubalen da suke fuskanta domin samo mafita
  • Sarkin Musulmin ya ba da wannan shawarar ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a fadarsa da ke Sokoto
  • Ya ba da tabbacin cewa sarakunan gargajiya za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya shawarci ƴan Najeriya da su rungumi tarin ƙalubalen da suke fuskanta, sannan su yi ƙoƙarin magance su.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar a fadarsa da ke birnin Sokoto.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya nuna babban kuskuren Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo

Sarkin Musulmi ya magantu kan rashin tsaro
Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro a Najeriya Hoto: Daular Usmaniyyya
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ambato Sarkin Musulmin yana cewa bai kamata mu bari a yi galaba a kan mu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ya yi murnar tarbar ministan tsaron na Najeriya a fadarsa.

Wace shawara sarkin Musulmi ya ba da?

"Mun ji daɗin tarbar shi a matsayin jami’in tsaro na ɗaya a ƙasar nan. Idan babu tsaro, ba za mu iya samun komai ba."
"Shi (Badaru) ya san nauyin da ke wuyansa. Na yi amanna cewa ya kasance yana tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin taimaka masa. Muna aiki hannu da hannu kuma ba za mu taɓa dakatar da yin hakan ba."
"Saboda yawan tattaunawa yana samar da maganin matsalolin da ake fuskanta. Tattaunawa ita ce hanya mafi sauƙi ta magance kowace irin matsala."
"Wannan ƙalubale ne amma na yi amanna cewa ƙalubale zai sanya mu zama mutane na gari. Mu rungumi tarin ƙalubalenmu, mu yi aiki domin magance su. Kada mu taɓa bari wani ya ci galaba a kan mu."

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC, ta hana su aikin majalisa

- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya ba da tabbacin cewa sarakunan gargajiya za su yi dukkanin mai yiwuwa domin ganin cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan.

Shawarar Sarkin Musulmi ga musulmai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya shawarci Musulmi da su nemi ilimin addinai da ba na su ba don samun zaman lafiya.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya kuma shawarci musulmai da su nemi ilimin sanin Ubangiji domin yin amfani da shi wurin zama mutane nagari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel