Satar Mazakuta: Menene Gaskiyar Batun Da Ya Zama Ruwan Dare a Sassan Najeriya
- An samu rahotanni da dama na satar mazakuta a baya-bayan nan a jihohin Najeriya kamar Nasarawa, Bauchi har ma da birnin tarayya Abuja
- Rundunar yan sandan Najeriya ta ja kunnen mutane su dena daukar doka a hannunsu idan ana zargin aikata laifi, maimakon hakan su kai rahoto wurin hukuma
- Likitoci da Legit Hausa ta tuntuba sun yi sharhi cewa batun sace mazakuta ba zai yi wu ba a likitance, sai dai akwai cututtuka da ka iya sanya mazakuta ta kankance
Batun satar mazakuta na daya cikin batutuwa da ke daukan hankulan yan Najeriya a cikin yan kwanakin nan, ko da ya ke mutane da dama na yi wa batun kalon almara.
Rahotanni da suka fito daga sassan Najeriya daban-daban ciki har da birnin tarayya Abuja sun nuna wasu mutane sun yi ikirarin an sace musu wannan sassan jikin ta hanyar asiri da ake kira 'shafimulera'.
Na baya-bayan nan a cikinsu shine wanda ya faru a ranar 8 ga watan Oktoban 2023 a Asaba, babban birnin Jihar Delta, inda fusatattun mutane suka afkawa wata dattijuwa mai shekara 60 da duka kan zargin sace mazakutar wani matashi mai suna Ebube Linus dan shekara 19 da suka shiga adaidaita sahu tare.
Dattijuwar ta yi sa'a jami'an tsaro sun taho wurin kafin a kai ga raba ta da ranta yayin da shi kuma wanda ya zarge tan ya gaza nuna hujjar cewa ta sace masa mazakuta, AIT ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya cigaba da cewa irin wannan abin da ya faru a Asaba ya yi kama da abubuwan da suka faru a sassan Najeriya kamar Nasarawa, Kano, Kaduna, Bauchi da Abuja da sauransu inda aka kai rahoton zargin satar mazakuta kimanin 200.
Yadda batun zargin satar mazakuta ke faruwa
Galibi ana zargin mutane da satar mazakutan ne bayan an yi musabaha ta hannu, ko an hada jiki ko ma shiga abin hawa tare da wani, daga nan sai kawai a ji ihun 'barawo' tare da cewa an sace al'aura.
Wani abin lura a nan shine dukkan wadanda ke ikirarin an sace musu al'aurar ba fa nufin suke babu al'aurar baki daya ba sai dai suyi ikirarin ta kankance ba yadda suka santa ba.
Tarihin zargin satar mazakuta a Najeriya
Daya daga cikin zargin satar mazakuta na farko-farko a Najeriya ya faru ne a shekarar 1975 a jihar Kaduna kamar yadda Dakta Sunday Elechukwu a cikin wata wasika da ya rubuta wa 'Transcultural Psychiatric Review'.
A cewar likitan kwalkwalwar an samu zargin satar mazakuta da dama a 1975 a sassan Najeriya da dama sai aka samu saukin abin sai ya sake dawowa a 1990. Bisa alamu har yanzu abin bai kau ba.
Martanin yan sanda kan satar mazakuta
Kwamishinan yan sandan Abuja Haruna Garba, a martaninsa kan lamarin ya ce zargin cewa mutane suna jin wani iri a jikinsu abu ne da ya dace a tabbatar a kotu yayin da ya ke gargadin mutane kan daukan doka a hannunsu.
Ya kara da cewa bisa alamu abin lamari ne da ya shafi kwakwalwa domin duk lokacin da aka tafi asibiti akan gano cewa al'aurar na nan.
"Wannan batun na satan al'aura ta maza kawai muka san ana yi duk da cewa a kwanakin baya wasu da na hadu da su sun ce min sun ji wata da aka sace mata nata kuma mamanta ya bace a Gwagwalada amma duk da haka ba mu da wata rahoto kan sace al'aurar mata.
Kuma ko na mazan ma da ake magana sashi fadi ne kawai, duk mutanen da ake yada rahoton cewa an dauke musu al'aura, an tafi asibiti an gwada su an gano cewa al'aurarsu lafiya kalau."
Abin da likitoci suka ce kan satar mazakuta
Legit Hausa ta tuntubi Dakta Nasir Ibrahim Kurfi, likita wanda ke kwarewa a bangaren tiyata da ke aiki a Asibitin Koyarwa ta Tarayya, FTH, da ke jihar Katsina don neman karin bayani kan batun satar mazakuta a likitance.
Dakta Kurfi ya ce sace wa dan adam al'aura abu ne wanda babu hujjan hakan ya taba faruwa a likitance. Ya kara da cewa akwai cututuka dai da kan iya sanya mazakutar mutum ta kankance amma hakan ma ba farat daya abin ke faruwa ba.
"Akwai cututtuka masu dangantaka da kwakwalwa ko tsananin damuwa kamar (acute panic anxiety attack, depression, schizophrenia, neurosyphilis ds) da ka iya sanya mutum ya ji kamar mazakutarsa ta bace ko kuma a samu kankancewar mazakutar."
Ya kara da cewa:
"Ba a taba kawo mana mutum a asibiti da cewa an sace masa mazakuta kuma min bincika mun tabbatar da hakan ba, don haka ba abu ne mai yiwuwa a likitance ba."
Wannan ya yi kamanceceniya da ra'ayin Dakta Bello Jami'u wanda ya ce:
"Akwai banbanci tsakanin sace mazakuta da kuma yanke mazakuta, abu ne mabanbanta, a kimiyyance, ba za a iya sace mazakuta ba idan dai ba tiyata aka yi aka yanke ta ba."
Asali: Legit.ng