Babbar Magana: Mataimakin Hafsan Tsaron Kasar Birtaniya Ya Shigo Najeriya
- Mataimakin babban hafsan tsaron Birtaniya, Laftanar Janar Sir Charlie Collins, ya isa Maiduguri domin karfafa hadin gwiwar tsaro da Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa wannan ziyara za ta ba shi damar ganin yadda kasashen biyu ke aiki tare wajen yaki da rashin tsaro
- Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar Najeriya da Birtaniya wajen yakar ta’addanci a yankin Sahel
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maiduguri, Nigeria - Mataimakin babban hafsan tsaron kasar Birtaniya, Laftanar Janar Sir Charlie Collins, ya isa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Babban jami'in tsaron Birtaniya ya kawo ziyara Najeriya ne domin tallafa wa kokarin inganta tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Source: Twitter
Hukumar Tsaron Birtaniya da ke kula da yankin Yammacin Afirka ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X a ranar Talata.
Ta bayyana cewa ziyarar za ta ba hafsan tsaron Birtaniya damar ganin yadda hadin gwiwar tsaro tsakanin kasarsa da Najeriya ke gudana a zahiri.
Birtaniya ta bayyana manufar ziyarar
A wani sako da ta wallafa, hukumar Birtaniya ta ce:
“Barka da zuwa Najeriya, Laftanar Janar Sir Charlie Collins KBE DSO, Mataimakin Babban Hafsan Tsaron Birtaniya.”
Ta ce jami’in yana Maiduguri tare da takwarorinsa na rundunar sojin Najeriya domin ganin yadda hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu ke gudana da tallafa wa kokarin da Najeriya ke jagoranta wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
Jawabin Bola Tinubu a kasar Birtaniya
Ziyarar Collins na zuwa ne watanni kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara kasar Birtaniya.
A lokacin wata liyafar girmamawa da aka shirya masa a St George’s Hall da ke Windsor Castle, Tinubu ya bayyana cewa hadin gwiwar Najeriya da Birtaniya na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Shugaban ya bayyana cewa dangantakar Najeriya da Birtaniya ta samo asali ne shekaru da dama da suka gabata ta fannoni da yawa, ciki har da dimokuradiyya, ilimi da kuma yan Najeriya da ke zaune a Birtaniya.

Source: Twitter
Hadin gwiwar Najeriya da Birtaniya
Ya bayyana cewa hadin gwiwa da Birtaniya na da matukar muhimmanci wajen fuskantar barazanar ta’addanci da ke addabar yankin.
“A kokarin da muke yi na yaki da wadannan barazana, hadin gwiwa da Birtaniya na da matukar muhimmanci,” in ji shugaban.
Ana sa ran ziyarar da mataimakin hafsan tsaron Birtaniya ya kawo tana da alaka da kokarin kara karfafa hadin gwiwa da Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya.
Sojoji sun ceto mutane 47 a Borno
A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun matsa wa 'yan ta'addan Boko Haram da kai hare-hare ta sama da kasa a maboyarsu da ke Borno.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun ceto mutane 47, wadanda yawancinsu mata ne da yara, daga hannun mambobin kungiyar ISWAP a jihar.
Sojojin sun ceto mutanen ne a gundumar Kangarwa da ke Karamar hukumar Kukawa a jihar Borno a wani aikin ceto da aka gudanar a ranar 20 ga watan Yunin 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

