Yadda Baba Ari Ya Nadawa Malamar Islamiyya Duka, Yayi Yunkurin Take Kanta da Takalmi

Yadda Baba Ari Ya Nadawa Malamar Islamiyya Duka, Yayi Yunkurin Take Kanta da Takalmi

  • Malama Zainab dake karantarwa a wata Islamiya a Unguwar Mubi dake Nasarawa a Kano ta zargi Baba Ari da lakada mata mugun duka
  • Kamar yadda aka tattauna da ita, tace tayi yunkurin hukunta diyar jarumin ne a Islamiyya yayin da suka yi laifi amma ta fadi cewa aljanu sun tashi
  • Jarumin barkwancin ya garzaya har Islamiyya kuma ya lakada mata duka har ta fadi kasa sannan yayi yunkurin take kanta da takalmi

Malamar makarantar Islamiyya a Unguwar Mubi dake kusa da Kofar Nassarawa a jihar Kano ta zargi jarumin barkwanci Aminu Baba Ari, da lakada mata duka har hakan ya kai malamar da faduwa kasa warwas.

Aminu Baba
Yadda Baba Ari Ya Nadawa Malamar Islamiyya Duka, Yayi Yunkurin Take Kanta da Takalmi. Hoto daga Aminu Baba Ari
Asali: Facebook

Fitaccen jarumin ya kara da yin barazanar take malamar da takalmi kamar yadda tace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: NAF Sun Sheke Rikakken Shugaban ‘Yan Bindiga, Ali Dogo

Malamar makarantar Islamiyyar mai suna Zainab ta sanar da Mujallar Fim yadda lamarin ya faru dalla-dalla.

Tace dalibai ne suka yi laifin da ya dace a hukuntasu kuma a ciki har da diyar Baba Ari wacce ana zuwa dukanta rike bulala tare da tsayawa kan cewa babu me dukanta.

A yayin kokarin dukanta ne ta fadi kasa kan cewa aljanunta sun tashi.

Malama Zainab ta kara da cewa:

“Bayan Aminu Baba Ari ya samu labarin, ya zo har makaranta inda ya lakada min duka har ina faduwa kasa. Daga nan yayi yunkurin taka ni da takalmi da.”

Saboda faruwar wannan al’amarin yasa hukumar makaranta suka nuna bacin ransu tare da daukar mataki ka wannan mummunan cin mutunci da aka yi wa malamarsu.

Sai dai a bangaren Aminu Ari, yace shi da bai lakadawa Malama duka ba kamar yadda ake yadawa. Ya san dai ya make dankwalinta ta baya.

Kara karanta wannan

Shekara 2 da Barin Ofis, Magu Ya Bayyana Dalili 1 da Ya sa Aka Fatattake Shi daga EFCC

“Kuma a halin yanzu an riga da an daidaita komai ya wuce.”

- Yace.

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani matashi a kofar Nasarawa dake jihar Kano mai suna Muhammad Bello, yace sun samu labarin yadda lamarin ya faru daga kannansu masu zuwa Islamiyyar.

Sai dai a halin yanzu an shawo kan lamarin tunda shi jarumin barkwancin yayi nadamar abinda ya aikata kuma an yi sasanci.

"Kun san daga 'dan fim yayi abu nan da nan za a yada shi balle kuma irin wannan abun kunyar. Hakan yasa duk lamarin ya yadu amma yanzu an yi sulhu tsakaninsu."

- Muhammad Bello yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel