Wasu 'Yan Mata 5 Sun Lakadawa Kawarsu Dukan Kawo Wuka Har Ta Mutu Kan 'Saurayi'

Wasu 'Yan Mata 5 Sun Lakadawa Kawarsu Dukan Kawo Wuka Har Ta Mutu Kan 'Saurayi'

  • Hukumar 'yan sanda reshen jihar Gombe ta kama wasu 'yan mata kawayen juna bisa zargin kisan wata kawarsu kan Saurayi
  • Kakakin 'yan sandan jihar, SP Abubakar, yace mahaifin wacce aka kashe ne ya kai rahoton yadda abun ya faru Caji Ofis
  • Rahoto ya nuna cewa matan su 5 suka tararwa Mamaciyar, suka lakata mata dukan tsiya, lamarin da ya yi ajalinta a Asibiti

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gombe - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Gombe ta bayyana wasu 'yan mata biyar ƙawaye da ta kama bisa tuhume-tuhume guda biyu, haɗa baki don aikata laifi da kuma kisan kai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar yan sanda na zargin 'yan mata da yin ajalin wata ƙawarsu kan 'Saurayi'.

Hukumar yan sanda a Gombe.
Wasu 'Yan Mata 5 Sun Lakadawa Kawarsu Dukan Kawo Wuka Har Ta Mutu Kan 'Saurayi' Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, yace wani Mutumi mai suna Yaya Ma'aji daga ƙauyen Chilo, ƙaramar hukumar Akko, ne ya kawo rahoton abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama wata malamar coci dake sayen yara kanana kan kudi N50,000

A cewarsa, a ranar 9 ga watan Satumba, 2022, mutumin ya kai rahoto gurin 'yan sanda cewa wasu kawayen ɗiyarsa, Munira Yaya, sun haɗa baki sun lakaɗa mata dukan kawo wuƙa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ASP Abubakar, ya ƙara da bayanin cewa shekarun 'yan matan da ake zargin ba zai wuce tsakanin 15 zuwa 16 ba.

Yace sakamakon wannan duka mai tsanani da suka mata, Munira yar shekara 18 ta jigata sosai, nan da nan aka gaggauta garzayawa da ita babban Asibitin Kumo, inda Likita ya tabbatar rai ya yi halinsa.

Meyasa ƙawayen suka yi ajalin ƙawarsu?

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan yace matan sun ɗauki matakin ne biyo bayan wani saɓani da ya shiga tsakanin su kan wani 'Saurayi'.

A bayanan SP Abubakar, "Bayan samun wannan rahoton jami'an yan sanda na Ofishin Akƙo suka garzaya wurin ka suka kamo waɗan da ake zargi."

Kara karanta wannan

Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

A wani labarin kuma Matashiyar Budurwar Najeriya Ta Wanke Kafa Har Turai Don Ganawa Da Baturen Da Ta Hadu Da Shi A Yanar Gizo

Wata matashiya yar Najeriya ta tafi kasar waje don yin ido hudu da baturen saurayinta ta kuma yada haduwar tasu a soshiyal midiya.

A cewar budurwar, ta hadu da baturen ne a dandalin kulla soyayya ta kasa da kasa kuma sun shafe tsawon watanni 6 suna soyewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel