Wata Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta

Wata Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta

  • Wata matar aure ta garzaya kotu domin neman a raba aurenta da mijinta wanda ya kwashe shekara 20
  • Matar auren ta koka kan yadda mijin nata ta takurawa rayuwarta wanda hakan har ya kai ga taɓa mata lafiya
  • Alƙalin kotun ta ƙi yarda ta raba auren ma'auratan amma dai ta zartar da wani hukunci a tsakanin su

Ibadan, Jihar Oyo- Wata matar aure ƴar kasuwa mai suna Tawakalitu Olayiwola, mazauniyar birnin Ibadan, ta nemi wata kotun kostomare da ta raba aurenta da mijinta na tsawon shekara 20 saboda mijin na yi mata sata da lakada mata duka.

Ms Olayiwola ta bayyana cewa ta yanke shawarar rabuwa da mijinta, Ganiu Olayiwola, saboda rayuwar ta na cikin haɗari a dalilin yawan hawan jinin da take samu. Rahoton Daily Nigerian

Kara karanta wannan

Wasa Da Rai: Bidiyon Wata Kyakkyawar Budurwa Cikin Zakuna Ya Janyo Cece-Kuce

Kotun
Wata Matar Aure Ta Nemi Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta Hoto: Punch
Asali: Twitter

A kalamanta:

“Maganar gaskiya, na fara hana shi muna haɗa shimfiɗa idan ya neme ni cikin dare saboda lokacin a gajiye nake."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A dalilin hakan sai ya riƙa ce min ina bin maza sannan ya cigaba da muzgunawa rayuwata."

Ta bayyana cewa tun shekarar 2003, abu kaɗan zata yiwa Mr Ganiu kawai sai ya hau ta da duka.

“Ya taɓa ƙoƙarin watsa min gubar acid a jiki wannan ne dalilin da ya sanya hawan jini ya kama ni."
“Ganiu bai taɓa zama mijin kirki da uba nagari a gare ni ba da ƴaƴan mu uku guda."
“Mai Shari'a, naira dubu kawai yake bamu ni da yara uku a matsayin kuɗin abinci cikin wata shida."
"Saboda rashin kulawar sa, na dage ina aiki tuƙuru domin ganin na riƙe gidan da ƴaƴan mu, amma Ganiu sai ya koma yana jin haushi na."

Kara karanta wannan

Buhari Na Tsaka Mai Wuya, Ƙungiyar Kwadugu Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Abu 2

Wanda ake ƙarar, wanda bai yi jayayya ba da ƙarar da ake masa, ya amsa cewa tabbas yana dukan matar sa saboda yadda a koda yaushe take dawowa gida cikin tsakar dare.

“Iyakar haƙuri nayi da Tawakalitu, sannan na gargaɗe ta har na shekara uku, amma ta cigaba da zama mara biyayya."
“A taƙaice idan taji ba zata iya cigaba da zama da ni ba, Olayiwola zata iya yin duk abinda ya kwanta mata a rai." Inji shi

An zartar da hukunci

Yayin da take yanke hukuncin ta, alƙalin kotu S.M. Akintayo, tayi nuni da cewa babu wani aure da za a raba a tsakanin Olayiwola da Ganiu.

Mrs Akintayo tayi bayanin cewa shaidun da suka gabata a gabanta sun nuna babu wani halastaccen aure a tsakanin su.

Ta ba mai shigar da ƙara kula da yaran a hannun ta sannan ta umurci wanda ake ƙarar da ya riƙa ɗaukar nauyin ciyarwa, karatu da maganin yaran.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Yi Watsi da Buhari da CBN, Ya Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsohon Naira a Jiharsa

Alƙalin ta kuma yi iyaka da hana Ganiu daga tsangwama, takurawa da yin katsalandan a cikin rayuwar Olayiwola.

Yan Sanda Sun Halaka Dan Ta'adda Sun Kwato Makamai a Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun samu gagarumar nasara a wani bata kashi da suka yi da ƴan ta'adda.

Ƴan sandan sun halaka wani daga cikin su yayin da suka kwato makamai a hannun su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel