2027: Salon Peter Obi Ya Fita Daban, Ya Bayyana Tsare-Tsarensa ga Najeriya

2027: Salon Peter Obi Ya Fita Daban, Ya Bayyana Tsare-Tsarensa ga Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya bayyana irin tsare-tsaren da tanadar wa Najeriya musamman kan tsaro
  • Tsohon gwamnan Anambra ya ce jajircewa da shugabanci mai inganci ne za su kawo ƙarshen garkuwa da mutane
  • Obi ya jaddada cewa idan yaƙi ya ɓarke bayan ya fita ƙasashen waje, zai dawo gida domin kare Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi ya jero tsare-tsaren da ya shirya wa Najeriya.

Peter Obi ya bayyana cewa a shirye yake ya mutu saboda Najeriya, yana mai cewa shugabanci na gaskiya yana buƙatar sadaukarwa domin ceto ƙasa daga matsalar tsaro.

Peter Obi ya sha alwashi kan tsaro a Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

Tsohon gwamnan Anambra ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da ɗan jarida Rufai Oseni a shirin Black Box na Nevon HQ, da aka wallafa a YouTube.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Yadda Obi ya shirya yaki da ta'addanci

An tambaye shi abin da zai yi a matsayin shugaban kasa domin ceto ɗaliban makaranta da aka yi garkuwa da su, da magance kashe malamai da manyan hafsoshin soja.

Ko da yake bai bayyana takamaiman dabarun soja ba, Obi ya ce jajircewa, ƙuduri da shugabanci nagari ne mabuɗin warware matsalar tsaro a ƙasar.

Ya ce lokacin da yake gwamnan Anambra ya yi yaƙi da masu garkuwa da mutane, kuma matakan da gwamnatinsa ta ɗauka sun sa ayyukan masu laifi suka ragu sosai.

Obi ya ambaci wani shahararren mai garkuwa da mutane mai suna Vance, wanda ya ce ya taɓa bayyana cewa aikata laifuffuka sun zama kusan ba zai yiwu ba a lokacin mulkinsa.

Ya ce dole ne gwamnati ta kasance mai cikakken iko, yana mai jaddada cewa ko gwamnati ce ta yi mulki ko kuma masu laifi, amma ba za su iya mulki tare ba.

Peter Obi ya bayyana tsare-tsarensa ga Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a NDC kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: UGC

'Zan sadaukar da rayuwata ga Najeriya' - Peter Obi

Kara karanta wannan

'Ni ne gatan Isra'ila': Trump ya fusata da lamarin Netanyahu a yaki da Iran

A cewarsa, idan mutum yana son jagoranci, dole ne ya kasance a shirye ya sadaukar da rayuwarsa, ya ce wanda ba ya shirye ya mutu saboda jagoranci ya kamata ya janye.

Da aka tambaye shi kai tsaye ko yana shirye ya mutu saboda Najeriya, Obi ya amsa da cewa, “Eh.”

Ya ƙara da cewa idan ya kasance a wata ƙasa kuma yaƙi ya ɓarke a Najeriya, zai dawo gida domin kare ƙasarsa.

Peter Obi ya nuna damuwa kan yadda masu dauke da makamai ke ƙalubalantar ikon ƙasa, yana mai cewa shugabanci nagari ne zai iya dawo da martabar rundunar sojin Najeriya a duniya.

Ya kuma tuna yadda sojojin Najeriya suka taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a ƙasashe kamar Liberia, Sudan da Kuwait, yana mai cewa abin da ake buƙata yanzu shi ne ƙudurin tinkarar rashin tsaro kai tsaye.

'Obi bai da maraba da Buhari' - Kuti

A baya, an ji cewa wani mai fashin baki kan harkokin siyasa ya bayyana cewa matsalolin Najeriya sun fi karfin mutum guda ɗaya duba da matsalar kasar.

Masanin harkokin siyasar nan, Sola Kuti ya bayyana cewa tsarin siyasa ne babban kalubalen da ke hana ci gaba a Najeriya.

Ya ce ko shugaba mai kyakkyawar niyya zai fuskanci cikas daga masu ruwa da tsaki da tsarin da ke hana sauye-sauye masu ma'ana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.