Kotu Ta Yanke wa Halima Umar Hukunci bayan Kama Ta da Makamai Masu Hadari a Filato

Kotu Ta Yanke wa Halima Umar Hukunci bayan Kama Ta da Makamai Masu Hadari a Filato

  • Kotu ta yanke wa wata mata, Halima Umar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali bisa mallakar tarin makamai ba bisa ka'ida ba
  • Matar dai ba ta wahal ta kotu ba, ta amsa wasu daga cikin laifuffukan da ake tuhumarta da su tun a ranar da DSS ta gurfanar da ita
  • Hukumar DSS ta kama Halima ne a jihar Filato dauke da harsasai 302 na bindigun AK-47, wanda ake zargin za ta sayar wa yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja karkashin Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta kama wata mata, Halima Haliru Umar da laifin mallakar makamai masu hadari ba bisa ka'ida ba.

Kotun ta yanke wa matar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan samunta da laifin mallakar harsasai 302 na bindigar AK-47 ba bisa ka’ida ba da yunkurin bayar da tallafi wajen aikata ayyukan ta’addanci.

Kara karanta wannan

NJC ta saurari koke koke kan alkali 256, ta ladabtar da wasu daga cikinsu

Kotu.
Gudumar da ake amfani da ita a kotuna a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wacce aka yankewa hukuncin ta amsa laifuffuka biyu daga cikin tuhume-tuhume hudu da Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar a kanta, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

DSS ta cafke Halima a Filato

Tun farko dai hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Halima Umar a gaban kotu ne a ranar 11 ga Maris, 2026 bayan kama ta da makamai da ake zargin za ta kai wa 'yan bindiga a jihar Filato.

Bayan gurfanar da ita, an sake duba bayanan laifuffukan da ke cikin tuhuma ta uku da ta hudu wadanda ta amsa laifinsu ba tare da bata lokaci ba.

Yadda Halima ta amsa laifuffuka a kotu

A hukuncin da ta yanke yau Juma'a, Mai Shari’a Yilwa ta bayyana cewa wacce ake tuhuma ta amsa laifuffukan da ke cikin tuhume-tuhume na uku da na hudu tun ranar da aka gurfanar da ita.

Ta kara da cewa bisa amincewar da ta yi da laifin, ta karbi dukkan bayanan da masu gabatar da kara suka gabatar ba tare da kawo wata hujja domin kare kanta ba.

Kara karanta wannan

Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara

Lauya ya nema wa matar sassauci

Bayan an same ta da laifi, lauyanta Hamza Dantani ya roki kotu ta sassauta hukuncin da za ta yanke mata, cewar rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a X

Dantani ya ce Halima ba ta taba aikata wani laifi a baya ba kuma tana nadamar abin da ta aikata, kuma ba ta bata wa kotu lokaci ba dangane da zargin da ake mata.

Lauyan ya bayyana wa kotu cewa wacce ake tuhuma uwa ce mai shayarwa wadda aka kama tare da jaririnta mai shekara guda, yana rokon kotu ta hada adalci da jin kai.

Halima Umar.
Katar da aka kaka da makamai, Halima Haliru Imar da dakarun hukumar DSS a bakin aiki Hoto: @zagazolamakama
Source: Twitter

Hukuncin da kotu ta yanke

Lauyan masu gabatar da kara, Caliistus Eze, ya shaida wa kotu cewa babu wani bayani da ke nuna cewa an taba hukunta Halima a baya.

Mai Shari’a Yilwa, wadda ta dakatar da zaman kotun na dan lokaci, daga baya ta dawo ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 20 kan tuhumq uku, sannan shekara guda kan tuhuma ta hudu.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure ministan Buhari shekaru 75 a gidan kaso kan badakalar N33.8bn

An gurfanar da mutane 20 kan ta'addanci

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shari'o'in wadanda ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Rahoto ya nuna cewa gwamnatin ta gurfanar da akalla mutane 20 da ake zargi da ta'addanci a gaban babbar kotun mai zama a Abuja.

Bayanai sun nuna cewa an girke jami'an tsaro a muhimman wurare da titunan zuwa kotun domin tabbatar da tsaro a lokacin shari'ar wadanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262