Hannatu Musawa: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Tsige Minista Kan NYSC, Ta Kawo Dalilai

Hannatu Musawa: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar Tsige Minista Kan NYSC, Ta Kawo Dalilai

  • Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi fatali da korafin da ke neman rusa mukamin Ministar Al'adu, Hannatu Musawa
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a James Omotosho shi ya yanke wannan hukunci inda ya ce korafin ya gaza ba da gamsassun hujjoji
  • Wannan hukunci na zuwa ne bayan shigar da kara kan kasancewar Musawa Minista duk da kasancewarta mai bautar ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin da aka shigar kan Ministar Al'adu, Hannatu Musawa.

Kotun ta yi fatali da karar da ake kan Musawa game da mukaminta na Minista kan matsalar rashin yin bautar ƙasa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Hannatu Musawa
Kotu ta yi fatali da korafin da aka shigar kan muƙamin Ministar al'adu, Hannatu Musawa. Hoto: @BarrHannatu.
Asali: Twitter

Wane hukunci aka yanke kan Hannatu Musawa?

Alkalin kotun, Mai Shari'a, James Omotosho ya bayyana cewa masu korafin sun gaza kawo shaidu masu karfi kan shari'ar, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Patrick Eholor da Thomas Marcus wadanda ke kalubalantar Musawa sun shigar da kara kan rashin kammala bautar ƙasa na Ministar.

A cikin takardar korafi mai lamba FHC/ABJ/CS/1198/23 sun maka Shugaba Tinubu da Ministan Shari'a da kuma Hannatu Musawa.

Sun shigar da korafin ne a ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2023 inda suke neman bahasi kan doka game da Musawa, cewar Daily Post.

Masu karar sun bukaci sanin ko kasancewar Musawa a Minista a lokaci guda kuma mai bautar ƙasa ya halatta bisa doka.

Hanntu Musawa: Kotun ta yi fatali da korafi

Alkalin kotun ya tabbatar da cewa dole sai mutum ya cika ka'idoji kafin zama Minista kuma ba za a nada mutum Minista ba har sai ya cancanci tsayawa takarar Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Omotosho ya ce sai mutum ya cika shekaru 30 da kuma mallakar takardun sakandare kafin neman takarar Majalisar Tarayya kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce mallakar takardar NYSC kari ne daga abubuwan da ake bukata, domin haka korafinsu ba shi da tushe inda ya yi fatali da karar.

Lauya ya magantu kan dambarwar Musawa

A wani labarin, kun ji cewa, Wani lauya, Festus Ogun ya bayyana cewa mutane ba su buƙatar satifiket din NYSC kafin a ba su muƙamin siyasa.

Ogun ya yi martani ne a kan dambarwar da ake yi kan matsayin kammala bautar ƙasa na Ministar Al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel