'Ubangiji Ya Nuna Ikonsa': Diezani Ta Yi Martani bayan Wanke Ta daga Zarge Zarge
- Tsohuwar minista, Diezani Alison-Madueke ta nuna farin cikinta bayan wata kotu a London ta wanke ta daga dukkan tuhume-tuhume
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa an wanke Diezani ne daga cin hanci da rashawa da aka shigar a kanta
- Tsohuwar ministar man fetur ta ce ita da iyalanta sun sha wahala da damuwa tsawon kusan shekaru 11 da shari’ar ke gudana a Birtaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, UK - Tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta yi magana bayan wanke ta daga zarge-zargen da ake yi mata na tsawon shekaru.
Diezani ta mayar da martani bayan wata kotu da ke London ta wanke ta daga tuhume-tuhumen cin hanci da aka shigar a kanta.

Source: Facebook
A wata hira da ta yi da News Central TV ta bayyana cewa har yanzu tana zaune a Birtaniya tun bayan fara shari’ar shekaru 11 da suka gabata.
Cin hanci: Diezani ta yi godiya ga Ubangiji
Da take magana bayan hukuncin, Alison-Madueke ta bayyana jin daɗinta tare da cewa ita da iyalanta sun sha fama da matsananciyar damuwa da wahala sakamakon shari’ar.
Kotun Southwark Crown da ke London a Birtaniya ta yanke hukuncin wanke tsohuwar ministar daga dukkan tuhume-tuhume, ciki har da karɓar cin hanci sau biyar da kuma haɗa baki wajen aikata cin hanci.
Ta ce:
"Ina matuƙar gode wa Ubangiji, lamarin ya kasance mai wahala sosai tsawon kusan shekaru 11, ya jawo damuwa ba gare ni kaɗai ba har ma ga iyalaina da abokaina.”
"Har da mahaifiyata mai shekaru 93 da ke Fatakwal da kuma ɗana sun fuskanci wahalhalu saboda wannan shari’a da aka shafe shekaru ana yi.”

Source: Depositphotos
Matsalar da Diezani ta shiga a baya
Alison-Madueke ta ce tafiyar ta kasance mai ƙalubale, amma ta ci gaba da yin imani cewa Allah yana cika alkawuransa kuma baya karya magana.
“Ubangiji zai ci gaba da kasancewa Ubangiji. Ba mutum ba ne da zai yi ƙarya. Idan ya yi maka alkawari, tabbas zai tabbatar da shi.”

Kara karanta wannan
N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi
- Diezani
Tsohuwar ministar ta kuma bayyana cewa ta yi aikinta gwargwadon iyawarta yayin da take riƙe da muƙaminta, tana mai cewa ta kasance mai ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora mata yadda ya kamata.
Ta jaddada cewa bayan shekaru kusan 11 da ta shafe a Birtaniya saboda shari’ar, hukuncin kotun ya kawo mata da iyalanta sauƙi da kwanciyar hankali.
Shari'ar Diezani: Sunan ministan Buhari ya fito
Mun ba ku labarin cewa an ji sunan Emmanuel Ibe Kachikwu a shari'ar Diezani Alison-Madueke kan zargin karbar rashawa wanda ya saba dokar Najeriya.
Ana zargin mutanen Diezani Alison-Madueke sun ba tsohon ministan man cin hanci a shekarar 2015 lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.
Ibe Kachikwu ya rike shugabancin kamfanin NNPC bayan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015 da ta gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
