Sarki Muhammadu Sanusi II Ya Umarci Rufe Wani babban Otal a Kano
- Sarki Muhammadu Sanusi II na Kano ya bayar da umarnin rufe wani otal bayan korafe-korafe da aka kai masarautar
- Majalisar Masarautar Kano ta ce an ɗauki matakin ne bayan nazari kan ƙorafe-ƙorafen al’umma suka kai wanda ke da muhimmanci
- Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin ya yaba da matakin, yana mai cewa mazauna sun nuna damuwa kan abubuwan da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayar da umarnin rufe wani otal da ake zargin ana badala.
Basaraken ya umarci rufe otal ɗin 'Stephrica Guest Palace' nan take, wanda ke Kureken Sani a ƙaramar hukumar Kumbotso ta Kano.

Source: Twitter
An fitar da wannan umarni ne ta hannun Majalisar Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Galadiman Kano, Aliyu Ibrahim Matawalle, cewar Tribune.
Korafe-korafen da al'umma suka yi kan otal
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an dauki matakin ne bayan nazarin ƙorafe-ƙorafen da al’umma suka gabatar.
Majalisar masarautar ta bayyana cewa an cimma matsayar rufe otal ɗin ne bayan an yi nazari sosai kan damuwar da mazauna yankin suka nuna game da ayyukan wurin.
Ta ƙara da cewa matakin yana da nufin warware matsalolin da al’umma suka gabatar tare da tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da bin doka a yankin.
Wata majiya daga cikin Majalisar Masarautar Kano ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan bincike kan ƙorafe-ƙorafen da mazauna Kureken Sani suka shigar.
Baya ga umarnin rufe otal ɗin, Sarkin ya kuma umarci mamallakin ginin da ya mayar da wurin makaranta ko asibiti domin amfanin jama'ar yankin.
Majalisar ta ce sauya amfani da ginin zuwa makaranta ko asibiti zai kawo fa'idodi masu ɗorewa ga mazauna, musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya.

Source: Original
Martanin yan yankin da aka rufe otal
Da yake martani kan lamarin, shugaban ƙungiyar ci gaban Kureken Sani, Malam Muhammad Sabi’u Yahaya, ya yabawa Sarkin Kano bisa wannan mataki.
Ya ce tun da farko mazauna yankin sun kai ƙorafi ga masarautar kan zargin wasu ayyuka masu tayar da hankali da suka shafi yara ƙanana a cikin otal ɗin.
Yahaya ya ce:
“Muna godiya ga Majalisar Masarautar Kano saboda sauraron korafe-korafenmu da kuma ɗaukar matakin da ya dace bayan gudanar da bincike.”
Rufe otal ɗin ya haifar da muhawara mai yawa a tsakanin mazauna yankin, yayin da mutane ke jiran yadda za a aiwatar da umarnin masarautar, cewar Dala FM Kano.
Haka kuma jama'a na sa ido kan makomar ginin da irin sabon amfani da za a yi da shi domin amfanin al’ummar yankin a nan gaba.
Sarki Sanusi II ya ba Abba shawara
A wani labarin, an ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar gaisuwar sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Muhammadu Sanusi II ya ba da shawara ga Gwamna Abba kan yadda yake tafiyar da gwamnatinsa wajen mulkin jihar Kano.
Mai martaba sarkin ya bukaci Gwamna Abba da ya dauki kwakkwaran mataki kan masu kokarin kawo cikas ga gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng

