"Ka Cika Hakuri": Sanusi II Ya Shawarci Gwamna Abba kan Mulkin Kano
- Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya kai ziyarar gaisuwar sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano
- Muhammadu Sanusi II ya ba da shawara ga Gwamna Abba kan yadda yake tafiyar da gwamnatinsa wajen mulkin jihar Kano
- Mai martaba sarkin ya bukaci Gwamna Abba da ya dauki kwakkwaran mataki kan masu kokarin kawo cikas ga gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Mai martaba Muhammadu Sanusi II, ya ba da shawara ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Muhammadu Sanusi II ya shawarci Gwamna Abba da ya yi maganin duk wani mutum da ke ƙoƙarin gurgunta gwamnatinsa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Sanusi II ya ba da wannan shawarar ne a lokacin gaisuwa ta al'ada ta taya murnar Sallah bayan Eid da ya kai wa gwamnan.

Kara karanta wannan
Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya
Ya jaddada cewa dole ne shugabanci ya haɗa adalci da iko, inda ya kafa hujja da ayoyin Alƙur'ani mai tsarki domin fito da ma'anar batunsa.
“A cikin Alƙur’ani mai tsarki, bayan Allah ya yi magana kan aiko da manzanni da litattafai masu tsarki, ya kuma ambaci ƙarfe, wanda malamai ke fassara shi da iko da ƙarfi. Adalci ba zai iya tsayawa ba idan babu waɗannan abubuwa guda biyu."
- Muhammadu Sanusi II
Sarkin ya yaba wa Gwamna Abba kan faɗaɗa makarantu, fannin lafiya, da shirye-shiryen jin ƙai na al'umma, amma ya yi gargaɗi game da mika ban-girma ga waɗanda ba su dace da shi ba.
“Idan ka girmama mutum mai mutunci, za ka samu amincinsa. Amma idan ka girmama wanda ba shi da mutunci, sai ya zama mai girman kai kuma ya raina ka."
- Muhammadu Sanusi II
Sanusi II ya bayyana cewa mutane da dama a yanzu suna kallon gwamnan a matsayin wanda ya cika yawan haƙuri da juriya.
“Saboda hargitsi da rashin tsari da ke faruwa a Kano, mutane suna tunanin suna da gwamna mai haƙuri sosai kuma kowa yana iya yin abin da ya ga dama."
“Shawarata gare ka a matsayin ɗan uwa ita ce ka tashi tsaye ka fuskanci wannan ƙalubale, kuma ka bari mutane su sani cewa akwai gwamnati a Kano. Idan mutum ya bi doka, a bar shi ya rayu cikin zaman lafiya. Idan kuma ya ƙi, ka hukunta shi.”
- Muhammadu Sanusi II
Sarkin ya ce martanin da taron jama'a suka bayar ya nuna irin goyon bayan da al'umma ke da shi na a ɗauki tsauraran matakai.
Ya yi alƙawarin ba da goyon bayan majalisar masarautar, inda ya jaddada cewa nasarar gwamnan tana da alaƙa da makomar Kano baki ɗaya.
Yayin da yake mayar da martani, Gwamna Abba ya gode wa Sarkin da majalisarsa, inda ya ba da haƙuri game da soke taron Hawan Daushe.
Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin kauce wa tashe-tashen hankula a lokacin bukukuwan.
“Ina so na tabbatar wa Mai Martaba da al'ummar Kano cewa tun lokacin da Allah ya yi ni gwamna, ban taɓa tsoron kowane ɗan adam ba face Allah."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Asali: Legit.ng
