Siyasar Kano: 'Dan Aminu Gwarzo Ya Kai Karar Mai Magana da Yawun Gwamna Abba

Siyasar Kano: 'Dan Aminu Gwarzo Ya Kai Karar Mai Magana da Yawun Gwamna Abba

  • Mujahid Aminu Abdussalam Gwarzo ya kai ƙarar Sunusi Bature Dawakin Tofa ga kwamishinan 'yan sandan Kano kan zargin ɓata sunan mahaifinsa
  • Ƙarar ta ce Sunusi Bature ya yi kalaman da suka danganta Aminu Gwarzo da karɓar “Awalaja” daga shugabannin ƙananan hukumomi 44
  • Lauyan mai ƙarar ya buƙaci rundunar 'yan sanda ta binciki lamarin tare da ɗaukar matakin doka kan zarge-zargen da Sanusi ya yi a taron siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano – Babban ɗan tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Mujahid Aminu Abdussalam Gwarzo, ya shigar da ƙara kan Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Rahotanni sun nuna cewa Mujahid Gwarzo ya yi karar mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf din bisa zargin ɓata suna.

Mujahid Aminu Abdussalam Gwarzo ya shigar da kara kan Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sanusi Bature Dawakin Tofa, Mai magana da yawun Gwamnan Kano (hagu) da Mujahid Aminu Gwarzo, dan tsohon mataimakin gwamnan Kano (dama). Hoto: Sanusi Bature D-Tofa, Mujahid Aminu
Source: Facebook

An kai ƙarar hadimin gwamnan Kano

An miƙa ƙarar ne ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano a ranar 17 ga Yunin 2026 ta hannun lauyan mai ƙarar, Barrista Nazifi Yusuf Gorondutse, in ji rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Ba makaranta ba ce,' An samu sababbin bayanai kan harin Boko Haram a Borno

A cikin takardar ƙarar, Mujahid Gwarzo ya nemi rundunar ‘yan sandan Kano ta binciki wasu kalamai da ake zargin Sunusi Bature ya yi a wani taron siyasa da aka gudanar a ranar 13 ga Yunin 2026.

Mai ƙarar ya ce kalaman sun shafi mahaifinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda tsohon mataimakin gwamnan Kano ne kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar NDC.

Abin da ke ƙunshe a takardar ƙarar

Takardar ƙarar ta yi zargin cewa Sunusi Bature ya danganta Gwarzo da karɓar abin da aka bayyana a matsayin “Awalaja” daga shugabannin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Haka kuma, mai ƙarar ya ce daga baya an yaɗa bidiyon jawabin a shafukan sada zumunta, lamarin da ya yi tasiri ga mutunci da martabar Gwarzo a idon jama'a.

A cewar mai ƙarar, kalaman na ɗauke da ɓatanci kuma suna iya jawo wa mahaifinsa raini da zubar masa da mutunci a tsakanin al’umma.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Lauyan mai ƙarar ya roƙi rundunar ‘yan sanda da ta gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa tanadin doka.

Aminu Gwarzo ya kalubalanci gwamnatin Kano ta kawo hujjar cewa ya karbi kudin kananan hukumomi
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tare da Aminu Gwarzo a wani taro. Hoto: @Kyusufabba
Source: Twitter

Sanusi Bature bai yi martani ba

Kara karanta wannan

Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu ya ba BUK da jami'o'i 2 kyautar motocin CNG a Kano

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Sunusi Bature Dawakin Tofa bai fitar da wata sanarwa ko martani a hukumance dangane da zarge-zargen da ke cikin ƙarar ba.

Yayin da ake wannan, shafin Gida Gida TV a Facebook ya ruwaito cewa a yammacin Litinin, Sanusi Bature D-Tofa ya jagoranci wani muhimmin taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga mazabun Dawaki Ta Gabas da Dawaki Ta Yamma a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

A taron da aka gudanar a gidan Sanusi Bature dake Dawakin Tofa, masu ruwa da tsakin sun jaddada cikakken goyon bayansu ga APC, tare da bayyana goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Yusuf.

Gwarzo ya soki Abba kan tsaron Kano

A wani labari, mun ruwaito cewa, dan takarar gwamnan Kano a NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kakkausar suka kan yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a jihar.

Ya ce hare-haren da ake kai wa al’umma a wasu ƙananan hukumomi sun nuna cewa rayuka da dukiyoyin jama’a ba sa samun kariya yadda ya kamata.

Kwamred Aminu Gwarzo ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankunan Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com