Binciken da Tinubu Yake Yi a CBN zai tona asirin barnar Buhari Inji Kanal Dangiwa

Binciken da Tinubu Yake Yi a CBN zai tona asirin barnar Buhari Inji Kanal Dangiwa

  • Umar Dangiwa bai ganin Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da ya yaki rashin gaskiya
  • Tsohon sojan ya soki gwamnatin da ta gabata, ya ce ba a taba barna a tarihi kamar a lokacin ta ba
  • Idan aka kammala binciken da ake yi a CBN, Kanal Dangiwa ya ce asirin mulkin Buhari zai tonu

Abuja - Kanal Umar Dangiwa mai ritaya ya na da ra’ayin cewa gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ta fi kowace tafka rashin gaskiya.

A wata hira da aka yi da shi a Sun, Kanal Umar Dangiwa mai ritaya ya zargi Muhammadu Buhari da jagorantar gwamnatin da ta fi barna a tarihi.

Tsohon gwamnan mulkin sojan ya ce an yi ta’adin ne ta karkashin wasu daidaiku da su ka rika juya madafan iko, ya kara da cewa asiri zai tonu yanzu.

Kara karanta wannan

Idan Na Ga N1bn Sai Na Sume Inji Tsohon Gwamnan da Ya Je Kurkuku a Kan ‘Sata’

Buhari
Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Asirin Buhari zai tonu a binciken CBN

Dangiwa ya ce binciken da ake yi a bankin CBN zai fallasa barnar da aka yi a gwamnatin baya ta hanyar canjin kudin kasar waje da tsarin noma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

The Cable ta rahoto tsohon sojan ya na cewa maganar a ce Muhammadu Buhari bai san da labarin rashin gaskiyar da aka yi a lokacinsa ba, zancen banza ne.

"DSS sun sanar da shi kuma an bada shawarar ya cafke Gwamnan CBN kuma ayi bincike. Amma masu amfana su ka hana saboda tsoron tona masu asiri.
Mutum ba zai yi kuskure ba idan ya ce Najeriya ta zama kasar da aka tafka rashin gaskiya a shekaru takwas.

- Kanal Umar Dangiwa

Yaudar da aka yi wa jama'a

A cewar Dangiwa, Buhari ya rika yin son kai wajen nade-naden mukamai, ya rika fifita wani bangare na kasar kuma ya yaudari ‘yan Najeriya kan mulki.

Kara karanta wannan

Hannatu Musawa da Ministoci 4 da Su ka Jawo Rudani a Cikin Kwana 15 a Ofis

Duk alkawarin bayyana kadarori da dukiyar da shugaba Buhari ya rika yi kafin ya hau mulki ba, bai cika su ba a ra’ayin tsohon gwamnan sojan na Borno.

"Maganar gaskiya a kan Buhari"

"Bayyana kadarorin da ya yi wa manoman Katsina ba ta da amfani kuma ba ta cika hurumin doka da tsammanin al’umma, bai nufin ya kara tsiyace a mulki.
Maganar gaskiya ita ce ya jagoranci gwamnatin da ta fi kowace tafka rashin gaskiya a tarihin kasar nan"

- Kanal Umar Dangiwa

Sojan ya soki wasu ayyuka 20 da aka yi a Daura, ya ce an yi ne saboda mahaifar shugaban kas ace ba tare da la’akari da amfanin da za su yi wa kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel