Zamfara: Kanal Dangiwa Ya Bayyana Hatsarin Da Ke Tattare Da Mallakawa Mutane Bindiga, Ya Bayyana Mafita

Zamfara: Kanal Dangiwa Ya Bayyana Hatsarin Da Ke Tattare Da Mallakawa Mutane Bindiga, Ya Bayyana Mafita

  • Kanal Shehu Dangiwa Umar, tsohon gwamnan mulkin soja na Jihar Kaduna ya nuna rashin amincewa da umurnin gwamnan Zamfara na cewa mutane su siya bindiga su kare kansu
  • Kanal Dangiwa ya ce hakan ba mafita bane domin bindigan da yan sanda za su iya bawa mutane ba su kai na masu garkuwar ba kuma bindigun na iya komawa hannun bata gari, laifuka su yi yawa
  • Tsohon gwamnan ya ce mafita kawai shine gwamnati ta kara yawan jami'an tsaro sannan a samar musu makamai da sauran kayan aiki a karfafa musu gwiwa su magance matsalar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon gwaman mulkin soja na Jihar Kaduna, Kanal Shehu Dangiwa Umar (mai ritaya), ya nuna rashin amincewarsa da umurnin da gwamnan Zamfara ya bada na cewa mutanen jiharsa su mallaki bindigu su kare kansu daga yan bindiga da masu garkuwa, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Hanyar da mazauna Zamfara za su bi su samu lasisin rike bindiga

Gwamnatin na Zamfara ta kuma umurci kwamishinan yan sandan Jihar ya bada lasisi ga duk wanda ya cika ka'idoji kuma yana son mallakar bindiga.

Kanal Dangiwa Umar da Shugaba Buhari.
Zamfara: Kanal Dangiwa Ya Bayyana Hatsarin Da Ke Tattare Da Mallakawa Mutane Bindiga, Ya Bayyana Mafita. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma Kanal Umar ya ce ya fahimci damuwar da gwamnonin arewa maso yamma ke ciki kan rashin tsaro, amma ya ce babu dalilin da zai sa 'su zauna a manyan biranen jihohinsu suna bada umurnin mutane su mallaki bindiga'.

Ya ce umurnin zai kara ingiza matsalar ne kuma bindigu su koma hannun bata gari.

"Wasu mutane za su siya bindigan ne ba don yaki da masu garkuwa ba amma don aikata laifi. Bindigan za su fada hannun wadanda ba su dace ba; kuma bindigan ma ba za su iya yakar masu garkuwar ba.
"Abu mai hatsari ne fada wa jami'an tsaro da shugaban kasa cewa mun cire tsammani da ku," in ji shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Ya yi karin bayani cewa bindiga mafi karfi da kwamishinan yan sanda zai iya bada lasisin mallaka shine 'double-barrel ko pump action, yana mai cewa nisan harbinsu daga mita 50 zuwa 100 ne yayin da yan bindiga ke amfani da AK-47 da AK-49 masu nisan mita 300-500.
"Ba za ka iya kare kan ka daga yan bindiga masu zuwa da AK-47 da AK-49 wasu lokutan ma da machine gun mai nisan mita 2,000. Don haka, damuwa ce ta saka gwamnan ya furta hakan amma ba zai mana amfani ba," in ji shi.

Kangiwa ya bada misali da Amurka inda bindiga ta zama musu matsala

Hakazalika, ya bada misali da Amurka inda a yanzu ta ke fama da matsalar hallastawa farar hula mallakar bindiga.

"Ta zama matsala ga Amurka kuma yanzu suna neman yadda za su warware matsalar kyalle kowa ya siya bindiga."

Menene mafita?

Kanal Dangiwa ya ce hanyar da ta fi dacewa a magance matsalar yan bindiga a arewa maso yamma shine gwamnati ta kara adadin jami'an tsaro ta kuma samar musu makamai da suka dace.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jihar Zamfara Za Ta Fara Yanke Wa Masu Garkuwa Da Yan Bindiga Hukuncin Kisa

"Muna bukatar karin jami'an tsaro don mafi yawancin dazukan arewa yan bindiga sunyi kaka-gida.
"Don haka muna bukatar karin jami'an tsaro su shiga dajin su fatattake su kuma a wadatar da su da makamai, wannan shine kadai mafita," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel