Yadda Tinubu Ya Gano Shirin Gwamnonin APC wurin Cire Shugabansu
- Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya zargi wasu gwamnonin APC da yin makarkashiya kan shugabansu a Najeriya
- Nwifuru ya yabawa Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya fi su dabaru kan wannan shiri, kuma ya dakile yunkurinsu na sauke Hope Uzodimma
- Ya ce masu shirin sun yi amfani da sunan Tinubu domin halasta matakinsu, amma sun gaza yayin da shugabancin Uzodimma ya ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya soki wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ake zargi sun yi ƙoƙarin cire Hope Uzodimma daga kujerar shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC ta (PGF).
Sai dai ya yabawa Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ya fi gwamnonin da suka yi tawaye dabaru, shirin da suka ƙulla.

Source: Facebook
Nwifuru ya yi wannan jawabi ne a wani gangamin masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abakaliki domin neman goyon bayan sake zaɓensa da kuma tazarcen Shugaba Tinubu, cewar Punch.
Makircin da aka kulla wa Gwamna Uzodinma
Ya yi iƙirarin cewa shirin da aka yi wa Uzodimma ya samo asali ne daga siyasa, kuma an danganta shi da Shugaba Tinubu ba tare da hujja ba.
A cewarsa, waɗanda ke bayan wannan yunkuri sun yi ƙoƙarin amfani da sunan shugaban ƙasa domin ba wa halasta matakinsu, amma sun kasa cimma burinsu.
Nwifuru ya ce lokacin da wasu suka haɗa kai domin yin aiki a kan jagoransu kuma shugaban PGF, Shugaba Tinubu ya nuna cewa ya fi su basira da dabara wajen tafiyar da siyasa.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka shirya sauke shugaban PGF sun yi ikirarin cewa shugaban ƙasa ne ya umarce su da yin hakan, amma hakan bai tabbata ba.

Source: Facebook
Kokarin da Tinubu ya yi a Kudu
Gwamnan ya jaddada cewa Uzodimma har yanzu shi ne shugaban PGF kuma jagoran APC a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kamar yadda TheCable ta ce.
Ya ce lokacin da Shugaba Tinubu ya ba yankin Kudu maso Gabas shugabancin PGF, gwamnonin APC biyu kacal ne ke yankin, kuma hakan ya nuna yana da muradun yankin a zuciyarsa.
Nwifuru ya nace cewa tsarin shugabanci a APC yana nan daram, tare da yaba wa salon jagoranci da dabarun siyasar Tinubu, yayin da ya sake tabbatar da matsayin Hope Uzodimma a matsayin shugaban PGF.
Rahotanni sun nuna cewa a makonnin baya PGF ta fuskanci rikicin shugabanci sakamakon saɓanin ra’ayi tsakanin wasu gwamnonin APC kan tsarin jagoranci da tasirin ƙungiyar a cikin jam’iyyar mai mulki.
Gwamna Nwifuru ya nemi afuwar talakawa
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya roki mazauna jihar da su yafe kura-kuran gwamnatinsa da na ’yan majalisar da aka zaba.
Bugu da kari, gwamnan ya yi kira ga jama'ar jihar Ebonyi da su sake bai wa jam’iyyar APC goyon baya a babban zaben shekarar 2027.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026 yayin wani taro da aka gudanar a wajen ibada na gidan gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

