Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban 'yan bindiga

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban 'yan bindiga

  • Rundunar yan sanda sun yi nasarar kama wata mai yi wa yan bindiga safarar makamai a jihohin arewa maso yamma da tsakiya
  • An kama Fatima Lawali ne mai shekaru 30 dauke da harsahi guda 991 na AK-47 za ta kai wa wani dan bindiga mai suna Ado Alero a Zamfara
  • Kwamshinan yan sanda CP Ayuba Elkanah ya ce an kwace makaman sannan tuni an fara bincike a kan lamarin idan an gama za a gurfanar da ita

Jihar Zamfara - 'Yan sanda a jihar Zamfara sun cafke wata mai shekaru 30, Fatima Lawali dauke da harsashi na bindigar AK-47 har guda 991, rahoton LIB.

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba Elkanah, yayin zantawa da manema labarai a yau Juma'a 26 ga watan Nuwamba.

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban 'yan bindiga
Hotunan makaman da aka kwato hannun masu taimakawa yan bindiga a Zamfara. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000

Ya ce wacce ake zargin tana kan hanya ne zuwa kai wa wani hatsabibin dan bindiga mai suna Ado Alero, wanda ya dade yana adabar mutanen Zamfara da kewaye.

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban 'yan bindiga
Wadanda ake zargi masu taimakawa yan bindiga ne da aka kama. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban 'yan bindiga
Fatima Lawali, matar da aka kama da harsashi 991 za ta kai wa shugaban yan bindiga. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kwamishinan yan sandan ya ce:

"A ranar 25 ga watan Oktoban 2021 misalin karfe 0930hrs, yan sandan rundunarsa da na FIB/STS karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba sun kama wata Fatima Lawali, yar asalin karamar hukumar Kauran Namoda wacce ta kware wurin yi wa yan bindiga safarar makamai a jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Katsina da Niger."

An kama ta a Gada Biyu da ke karamar hukumar Bagudu dauke da harsashi dari tara da casa'in da daya (991) na bindigar AK-47 za ta kai wa shugaban yan bindiga mai suna Ado Alero a kauyen Dabagi a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Hakazalika, Elkanah ya ce ana cigaba da gudanar da bincike a game da lamarin.

Na yi farin ciki da aka kama ni, na san laifi na ke yi, in ji mai kaiwa 'yan bindiga bayanan sirri a Zamfara

Hatsabibin mai kai wa 'yan bindiga bayannan sirri, Babuga Abubakar ya amsa cewa shine ya gayyaci 'yan bindigan su kai hai kauyen Wanke a karamar hukumar Gusau domin su sace wasu shanu 240.

Rundunar yan sandan Zamfara tare da rundunar FIB/STS daga hedkwata a Abuja karkashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, a baya sun yi holen wanda ake zargin a Gusau, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara Mr Ayuba Elkanna ya ce an kama wanda ake zargin ne da taimakon bayyanan sirri da aka samu game da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel