An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri
- Sojan Najeriya ya shiga hannun hukuma bayan an kama shi da harsashi fiye da 2000 a tashar Maiduguri
- Sojan ya shaidawa yan sanda cewa ya samu harsashin ne daga wata mota a wajen aikinsa
- Rundumar sojoji na jiran a mika mata jami'in don gudanar da cikakken bincike a kansa
An kama wani jami'in sojan Najeriya, Sani Mohammed, da akwati biyu na harsashi 2000, wanda suka tabbatar da lamarin sun shaidawa Premium Times.
Sojan, mai mukamin lance corporal, ya shiga hannu a tashar Maiduguri inda ma'aikatan NURTW suka kama shi lokacin da ya ke shirin hawa mota don tafiya babban birnin tarayya, Abuja.
Hoto
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda
Kamar yadda majiyar mu ta ruwaito, sojan, wanda ke cikin tawagar jami'ai na musamman 198, an sallame shi daga aiki a Damasak da ke Jihar Borno bayan ya samu rahoton jinya.
Da yan sanda suke tuhumar sa, Mohammed ya ce ya samu harsahin daga wata mota da ta lalace a wajen aikin sa.
Sauran abubuwan da aka samu a wajen Lance Corporal Sani Mohammed bayan harsashi 2000 sun hada da shaidar hutun aiki na kwana uku da kuma takardun gwajin asibiti guda biyu. Rundunar soji ta ce sojan bai karbi izinin yin tafiya ba.
Wata majiyar sojoji ta ce rundunar soji na jiran hukumar yan sanda ta mika mata jami'in don gudanar da cikakken bincike akan lamarin.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo
Mai magana da yawun yan sandan Jihar Borno, Edet Okon, ya ce zai gana da manema labarai dangane da batun a Maiduguri. Shima mai magana da yawun rundunar soji Frank Mba bai daga waya ko ya dawo da martanin sakon da aka yi masa ba.
A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.
Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.
Asali: Legit.ng