Bayan Kotu Ta Nemi a Soke ADC, Tinubu Ya Yi Kira ga Alkalai

Bayan Kotu Ta Nemi a Soke ADC, Tinubu Ya Yi Kira ga Alkalai

  • Shugaba Bola Tinubu ya umarci bangaren shari’a na Najeriya da ya tabbatar da an yi adalci cikin gaggawa kuma ba tare da nuna bambanci ba
  • Bola Tinubu ya jaddada cewa gurɓataccen tsarin shari’a na iya barazana ga dorewar dimokuraɗiyya a Najeriya da cigaban kasar gaba daya
  • Maimakon ci gaba da fuskantar korafe-korafen jama’a kan jinkirin sauraron shari’u da tara ƙararraki, ya ce dole ne a rika aiki cikin adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci alkalan kotun ɗaukaka ƙara na ƙasar da su rika adalci da shari'a cikin sauri, gaskiya kuma ba tare da la’akari da matsayin mutum, ƙabilarsa ko dukiyarsa ba.

Tinubu ya bayyana cewa rashin gyaruwar tsarin shari’ar kasar zai kasance barazana ta kai tsaye ga zaman lafiya da dimokuraɗiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a Ukraine bayan Rasha ta harba daruruwan jiragen yaki

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Tinubu ya yi wannan kira ne yayin ƙaddamar da sabon ginin kotun daukaka kara a Abuja da ke Dakibiyu.

Dalilin fadada kotu a Abuja

Shugaban ƙasar, wanda Sanata Kashim Shettima ya wakilta a wajen ƙaddamar da aikin, ya yaba da kammala ginin kotun da ya maye gurbin tsohon wurin da ya bayyana a matsayin mai ƙunci kuma na wucin gadi.

Shettima ya bayyana cewa Tinubu ya ce aikin wani ɓangare ne na cika alkawuran Ajandar Renewed Hope ta dawo da martabar cibiyoyin shari’a a Najeriya.

Kiran Shugaba Bola Tinubu ga alkalai

A cikin wata sanarwa da hadimin Shettima, Stanley Nkwocha, ya wallafa a X a ranar Litinin, an ruwaito Tinubu yana cewa:

“Ga alkalanmu, yayin da ku ke komawa wannan sabon gini, Najeriya na roƙon abu ɗaya daga gare ku: ku tabbatar kun yi hukunci da adalci cikin sauri.

Kara karanta wannan

Janar Rabe: Buratai ya yi gargadi kan 'sace' gwamnoni da ministoci a Najeriya

"Ya kasance cikin gaskiya. Ya kasance ba tare da la’akari da matsayi, ƙabila ko dukiya ba. Talaka ya ji cewa wannan kotu ita ce mafakarsa ta ƙarshe.”

Abin da sabon ginin ya kunsa

Rahotanni sun bayyana cewa sabon ginin kotun daukaka karar ya ƙunshi manyan ɗakunan shari'a guda biyu da ƙanana guda takwas.

Shugaban ƙasar ya ce sabon gini zai taimaka wajen hanzarta yanke hukunci, rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma ƙara amincewar jama’a da doka.

“Da manyan ɗakunan kotu guda biyu da ƙananan guda takwas, yanzu za a ba wa shari’u kulawa cikin sauri."
Kotun daukaka kara a Abuja
Sabon ginin kotu da gwamnatin Bola Tinubu ta yi. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Kotu nemi a soke rajistar ADC

A wani labarin, mun kawo muku cewa mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin soke rajistar jam’iyyar ADC.

Baya ga ADC, kotu ta hada da wasu jam’iyyu huɗu bisa zargin gaza cika sharudan kundin tsarin mulki da ake buƙata domin ci gaba da kasancewa da rajista.

Ƙarar da kungiyar tsofaffin ’yan majalisu ta kasa ta shigar, na neman kotu ta tilasta wa INEC cire ADC, AA, APP, jam'iyyar Accord da ZLP daga kundin rajistar jam’iyyun siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng