1448: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

1448: Sarkin Musulmi Ya Sanar da Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 a Najeriya bayan ganin wata a yammacin ranar Litinin
  • Sanarwar da fadar Sarkin Musulmi ta fitar ta nuna cewa yau Talata, 16 ga Yunin 2026 ne ta kasance 1 ga watan Muharram na shekarar 1447
  • Wasu jihohi a Arewacin Najeriya sun bayar da hutu domin ba al'ummar Musulmi damar yin bikin sabuwar shekarar ba tare da cikas ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026, a matsayin ranar farko ta Muharram 1448AH.

Sanarwar ta nuna cewa ranar Talata ce farkon sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan kammala shekarar 1447 a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto matar Janar Rabe Abubakar bayan artabu da ‘yan bindiga a Katsina

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III
Mai Alfarma Sarkin Musulmi a hagu, jinjirin wata a gefen dama. Hoto: Sultanate Council Sokoto Public Relations Unit|Getty Images
Source: UGC

Legit Hausa ta tattaro bayanin Sarkin Musulmi game da shiga sabuwar shekarar ne a wani sako da fadar shi da ke Sokoto ta wallafa a Facebook.

An shiga sabuwar shekarar Musulunci

Shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanar da shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 a Najeriya.

A cewar sanarwar, an ayyana shiga sabuwar shekarar ne bayan an ga jinjirin watan Muharram a sassa daban-daban na ƙasar nan tare da amincewar Majalisar Masarautar Sakoto da rahotannin da aka gabatar.

Sarkin Musulmin ya taya Musulmi a faɗin Najeriya da duniya murnar sabuwar shekarar Musulunci, sannan ya buƙace su da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a, yin nazari da ƙara ƙaimi wajen bin koyarwar addinin Musulunci.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya, tsaro da ci gaban ƙasa. Muharram shi ne wata na farko a kalandar Musulunci, kuma yana daga cikin watanni huɗu masu alfarma a Musulunci.

Kara karanta wannan

1448AH: Gwamna Abba ya ba da hutun sabuwar shekarar musulunci a jihar Kano

An ba da hutun 1448 a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ayyana ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hadimin Gwamna Umar Namadi, Ismaila Ibrahim Dutse ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa hutun zai bai wa ma’aikata da sauran al’umma damar shiga cikin bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci.

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi na bayani a wajen taro. Hoto: Garba Muhammad
Source: Twitter

Sanarwar ta ƙarfafa dukkan ma’aikata da al’ummar Jihar Jigawa da su yi addu’o’i domin dorewar zaman lafiya da ci gaba a faɗin jihar.

Ta ce:

“Yana da matuƙar muhimmanci ga dukkan ’yan ƙasa su kasance masu bin doka da oda tare da gujewa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Jigawa.”

Bayan Jigawa, an samu rahoton bayar da hutun shiga sabuwar shekarar 1448 a jihar Kebbi da ke Arewa maso Yamma.

An ba bada hutun shiga 1448 a Kano

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta dauki matakin farko bayan mutuwar Janar Rabe a Katsina

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu na musamman bayan shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ayyana hutun ne a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin 2026 domin ba jama'ar jihar damar yin bikin shiga sabuwar shekarar.

An bukaci jama'ar Kano da su gudanar da addu'o'i domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar a lokacin bikin shiga sabuwar shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng