NBS: Farashin Tumatur, Masara, Albasa da Wasu Kayan Abinci Ya Tashi a Najeriya
- Hukumar kididdiga ta kasa ta ce hauhawar farashin kaya a Najeriya ta tashi daga 15.69% zuwa 15.93% a watan Mayun 2026
- Farashin kayan abinci kamar albasa, masara, tumatir da doya sun taka rawa wajen tashin farashin abinci a fadin kasar nan
- Jihohin Yobe, Anambra da Sokoto ne suka fi fama da hauhawar farashi yayin da Niger da Plateau suka samu saukin hauhawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa alkaluman hauhawar farashin kaya a Najeriya sun karu zuwa kashi 15.93 a watan Mayun shekarar 2026.
Rahoton hukumar ya nuna cewa adadin ya karu da kashi 0.24 idan aka kwatanta da watan Afrilu da aka samu kashi 15.69.

Source: Getty Images
Hauhauwar farashin kaya a Najeriya
Sai dai idan aka kwatanta da watan Mayun shekarar 2025, an samu raguwar kashi 10.13 daga kashi 26.06 da aka samu a lokacin, in ji rahoton Daily Trust.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ne mafi girman hauhawar farashi da aka samu tun bayan watan Disamban da ya gabata lokacin da farashin kaya ya fara sauka a hankali.
A cewar NBS, hauhawar farashi daga wata zuwa wata ta tsaya a kashi 1.75, wanda ya ragu idan aka kwatanta da kashi 2.13 da aka samu a watan Afrilu.
Hukumar ta ce hakan na nufin saurin tashin farashi a watan Mayu ya ragu idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci daga wata zuwa wata ta tsaya a kashi 2.98, wanda ya ragu da kashi 0.65 idan aka kwatanta da watan Afrilu.
A bangaren shekara zuwa shekara kuwa, farashin kayan abinci ya kai kashi 16.96, yayin da a watan Mayun 2025 ya kai kashi 24.55.
Kayan da suka kara tsada
NBS ta danganta tashin farashin abinci da karin kudin wasu muhimman kayan masarufi da suka hada da albasa, masara, egusi, rogo, barkono, tumatir, dawa, doya da dankali.
Sauran kayayyakin sun hada da ayaba, wake, citta da kifi busasshe, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
Hukumar NBS ta ce matsakaicin hauhawar farashin abinci na watanni 12 zuwa Mayun 2026 ya tsaya a kashi 16.99.
Wannan ya nuna raguwar 16.22% idan aka kwatanta da 33.21% da aka samu a shekarar 2025.
Jihohin da suka fi fama da hauhawar farashi
Rahoton ya nuna cewa jihohin Yobe, Anambra da Sokoto ne suka fi samun hauhawar farashi idan aka duba shekara zuwa shekara.

Source: Facebook
Yobe ta samu kashi 24.94, Anambra kashi 23.29, yayin da Sokoto ta samu kashi 22.60. A daya bangaren kuma, jihohin Niger, Plateau da Edo ne suka fi samun saukin hauhawar farashi.
Benue, Bayelsa da Borno sun fi samun karin farashi idan aka duba daga wata zuwa wata, yayin da Niger, Zamfara da Taraba suka samu sauki.
A bangaren farashin kayan abinci kuwa, jihohin Adamawa, Kwara da Rivers ne suka fi samun tashin farashi idan aka kwatanta da bara.
Sai dai jihohin Borno, Taraba da Bayelsa sun samu mafi karancin tashin farashin kayan abinci a kasar.

Kara karanta wannan
Sauki ya zo: Matatar Dangote ta rage farashin man fetur bayan yarjejeniyar Amurka, Iran
Farashin buhun shinkafa ya tashi
A wani labari, mun ruwaito cewa, NBS ta bayyana cewa a binciken da ta gudanar a watan Maris, 2026, farashin buhun shinkafa 50kg ya tashi da kashi 20.5.
Rahoton na NBS ya nuna cewa matsakaicin farashin buhun shinkafar ya kai N112,000 a watan Maris, daga N92,946 da aka sayar a watan Fabrairu
Sai dai binciken da aka yi ya nuna farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya dawo N60,000 a wasu kasuwanni a sassan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

