Hukumar INEC Ta Dauki Darasi, Ta Sauya Tsarin da Za Ta Yi Amfani da Shi a Zaben 2027
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ta sauya tsarin gudanar da ayyukanta ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026
- Ya bayyana cewa hukumar ta cire bayanan masu zaɓe sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba, inda ta bar akalla miliyan 100 da aka tantance
- Amupitan ya ce INEC ta sayo sababbin na'urorin BVAS guda 57,000 tare da inganta tsarin tura sakamakon zaɓe ta intanet domin ƙara gaskiya da sahihanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Joash Amupitan, ya ce hukumar ta sauya tsarin gudanar da ayyukanta ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026, gabanin babban zaɓen 2027.
Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne ta bakin kwamishiniyar hukumar ta ƙasa, May Agbamuche-Mbu, a ranar Talata a Abuja, yayin wani taron zaman lafiya da tsaro.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa an yi wa taron taken “Kare Zaman Lafiya da Ƙarfafa Haɗin Kan Al'umma a Yanayin Siyasa Mai Gasa”, wanda gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya.
INEC ta sauya tsarin gudanar da zabe
Ya bayyana gudanar da zaɓe da INEC ke yi a matsayin “muhimmin ginshiƙi wajen samar da zaman lafiya”.
Ya ce:
“Ba za mu iya ƙarfafa yardar mutane da INEC ba sai mun gane cewa babban zaɓen 2023 ya haifar da babban gibi kan yadda aka aminta da hukumar. Sai dai ana samun amincewa ne ta hanyar yadda ake gudanar da ayyuka.”
“A cikin watanni 13 da suka gabata, INEC ta yi amfani da zaɓukan gwamna da aka gudanar a wasu lokuta a jihohin Anambra, Ekiti da Osun, zaɓukan ƙananan hukumomin Abuja da na cike gurbi guda 16 a matsayin gwajin gano matsaloli da gyara su.
"Hakan ya ba mu damar kammala zaɓe tare da bayyana sakamako cikin sa'o'i 24. 'Yan ƙasa na buƙatar tabbataccen tsari, gaskiya da riƙon amana. Ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026, mun sauya tsarin gudanar da ayyukanmu.”

Kara karanta wannan
Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya
INEC ta tantance rijistar masu zaɓe
Amupitan ya ce ta hanyar ci gaba da yi wa masu zaɓe rajista da kuma amfani da tsarin tantance bayanai ta na'urar zamani (ABIS), hukumar ta cire bayanan rajistar sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba.
Ya ce hakan ya bar masu zaɓe sama da miliyan 100 da aka tantance, ciki har da mutane 232,658 masu buƙata ta musamman, waɗanda hukumar ta tanadar wa ƙarin na'urori da kayan taimako domin sauƙaƙa musu kaɗa ƙuri'a.
Amupitan ya ce hukumar INEC ta kuma inganta kayan aikin zaɓe tare da shirin gudanar da zaɓen gwaji a ranar 28 ga Nuwamba, 2026.
Ya ce:
“Maimakon amfani da fasahar da ba a gwada ba, mun sayo sababbin na'urorin BVAS guda 57,000, mun samar da wuraren ajiya masu kula da yanayin zafi a faɗin ƙasar, sannan mun rage adadin masu zaɓe da ake ware wa kowace na'ura daga 1,250 zuwa 850.”
Da gaske shugaban INEC zai yi murabus?
Kun ji cewa hukumar zaɓe ta INEC ta ce rahoton da ke cewa shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, zai yi murabus ƙarya ne.
Hukumar ta bayyana iƙirarin, wanda aka yaɗa tare da hoton da ke ɗauke da labarin a intanet, a matsayin ƙirƙirarren bayani da aka shirya domin yaudarar jama’a.
Asali: Legit.ng

