Ko ka san an taba daure Marigayi Sardauna a gidan yari
- Za ku ji yadda Firimiyan Arewa Ahmadu Bello yayi zaman gidan yari
- An daure Alhaji Ahmadu Bello ne a lokacin yana Hakimin Garin Gusau
- Daga baya dai aka fito da Marigayi Shugaban na Arewa daga gidan maza
Labari ya zo mana daga Jaridar nan ta Daily Trust ta Hausa watau Aminiya game da yadda aka daure Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello a shekarun baya.
An daure Sardana ne a lokacin yana Hakimi a Kasar Gusau inda aka zarge sa da handame kudin Hukuma. Sai dai masana tarihi sun ce asali rigimar sarauta ce ta barke tsakanin Ahmadu Bello da ‘Dan uwan sa Sarkin Musulmi Sir Abubakar na III.
KU KARANTA: Siyasar Kano: Rikicin Kwankwaso da Shekarau
Bayan an yankewa Sardauna daurin watanni 6 ne ya aikawa Marigayi Nnamdi Arzikwe takarda inda ya nemi ya sama masa Lauya. Amma sai da Sardauna ya nemi gudumuwar kudi daga hannun ‘Yan uwan sa ‘Yan Sarauta domin a sama masa Lauya a Kotu.
Iyan Zazzau Aminu da kuma Ciroman Kano Muhammadu Sanusi I da kuma irin su Malam Aminu Kano su ka taimakawa Gamji ya bar gidan yari. Daga baya ya sakawa Iyan Zazzau da Sarautar Sarkin Zazzau ya kuma godewa abokin adawar sa Malam Aminu Kano.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng